Wata majiya mai tushe ta tseguntawa Aminiya cewa jihohi 36 har da babban birnin tarayya na Abuja sun gabatar da sunayen mutum 108 ga Shugaba Muhammadu Buhari don ya ba su mukaman ministoci da shugabannin ma’aikatun gwamnati.
Hakan na zuwa ne bayan kwanaki 41 da shugaban ya bayyana aniyarsa ta fadada majalisarsa tare da nada sabbin shugabannin hukumomin gwamnati don ya dadadawa ’yan jam’iyyar da suka yi fushi.