Gwamnan Jihar Oyo Abiola Ajimobi da na Kano Andullahi Umar Ganduje da na Sakkwato Aminu Tambuwal da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da wasu manyan kasa ne suka hadu a Jihar Legas domin murnar zagowar ranar haihuwar Tinuba, inda ake shirya taro na musamman da ake kira Tinubu Colloqium.
Wannan taron shi ne karo na 10 da tsohon gwamnan na Jihar Legas ya shirya, sannan kuma ya zama dan shekara 66 ke nan a duniya.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada Alafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi da Ooni na Ife Oba Enitan Ogunwusi da sarkin Legas Oba Riliwanu Akiolu da tsohon shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu da sauransu.