✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnoni 7 da suka gaza kai bantensu Majalisar Dattawa

Gwamnonin sun sha kaye a hannun abokan karawarsu.

A halin yanzu akwai gwamnoni bakwai masu ci da suka gaza samun nasarar zabensu zuwa Majalisar Dattawa a zaben da ya gudana a karshen mako.

Gwamnonin dai sun gaza kai bantensu sakamakon shan kayen da suka yi a hannun abokan karawarsu.

Wadannan gwamnoni sun hada da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Ben Ayade na Jihar Kuros Riba da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu da kuma Darius Ishaku na Jihar Taraba.

Sauran sun hada da Darakta Janar na yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu, wato gwamnan Jihar Filato Simon Lalong da takwaransa na Jihar Benuwe, Samuel Ortom.

Wasu daga cikin tsoffin gwamnonin da suka rasa damar komawa Majalisar Dattawan sun hada da Kabir Ibrahim Gaya na Jihar Kano da Tanko Almakura na Jihar Nasarawa, da Gabriel Suswam na Benuwe da Sam Egwu na Ebonyi.

Akwai kuma tsoffin gwamnoni irinsu Ibrahim Hassan Dankwambo da Abdulaziz Yari da Godswill Akpabio da suka samu nasara.

Daga cikin wadanda suka samu nasara kuma akwai David Umahi na Jihar Ebonyi da Abubakar Sani Bello na Jihar Neja.

Masana na bayyana sakamakon wannan zabe a matsayin yadda jama’a suka nuna fushinsu kan rashin gamsuwa da ayyukan da wadannan mutane suka yi wa jama’a a wa’adin mulkinsu da ke shirin karewa.