✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Zamfara ta tsayar da ranar zaben kananan hukumomi

Hukumar Zabe ta Jihar Zamfara ta sanar da ranar Asabar, 5 ga watan Dasumban 2020, a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben majalisun…

Hukumar Zabe ta Jihar Zamfara ta sanar da ranar Asabar, 5 ga watan Dasumban 2020, a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben majalisun kananan hukumomin jihar.

Sanarwar ta biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar, Alhaji Bello Muhammed Matawalle ya bayar, cewa hukumar ta tabbatar ta shirya zaben kananan hukumomin ba tare da bata lokaci ba.

Kafin shigowar mulkin Jam’iyyar PDP a jihar, tsohuwar gwamnatin APC ta gudanar da zaben amma Majalisar Dokokin Jihar ta kori zababbun shugabannin kan zarginsu da yi wa dokokin kasa karan-tsaye musamman a yakin da jihar ke yi da matsalar tsaro.

Sanya ranar zaben na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren Hukumar, Muhammad Sani Halilu Kura da aka raba wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar.

Shugaban Hukumar, Alhaji Garba Muhammad Danburan Gusau, ya ce yana farin cikin shaida wa jama’a da dukkan jam’iyyun da ke da rajista da masu neman shiga zaben kananan hukumomi da jami’an tsaro da kafafen watsa labarai da dukkan masu ruwa da tsaki cewa an tsayar da 5 ga Disamban bana ta zama ranar zaben kananan hukumomi.

Danburan Gusau ya nemi goyon bayan jama’a da masu fada- a-ji, da sauran masu ruwa da tsaki, domin su gadanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.