A daidai lokacin da al’ummar Nijeriya ke ci gaba da dandana kudarsu kan karin kudin man fetur sakamakon janye tallafin mai da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi da kuma janye tallafin aikin Hajji da ya jawo kudin kujera ya haura Naira miliyan takwas, sai ga shi gwamnatin ta kara kudin wutar lantarki da ninki uku a karkashin shirinta na janye tallafi.
Duk da cewa gwamnatin Tinubu ta ce karin kudin wutar lantarki ya shafi masu amfani da ita da suke Rukunin A, (Band A) ne, ’yan Najeriya da dama sun nuna rashin amincewa da fara amfani da karin da suke ganin marar kan gado ne, saboda kamfanonin rarraba wutar lantarkin ba su tsaya sun tantance rukunan masu amfani da wutar ba suka shiga aiwatar da tsarin.
Sun ce wadanda ba su samun wutar ta awa 20 an gwama su da masu samunta aka yi musu kudin goro wajen amfani da sabon farashin.
- Kamfanonin jiragen sama sun koka kan karancin fasinjoji
- Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar gasar LaLiga
Lamarin ya janyo hatsaniya da kin amincewa da korafe-korafe, inda masu amfani da lantarkin suka ce da gangan kamfanonin rararba wutar lanatarkin suka yi haka don su cuce su.
A ranar Larabar makon jiya ne Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta bayar da sanarwar karin kaso 300 (ninki uku) da mutanen da ke Rukunin A, za su rika biya, karin ya tashi daga kan Naira 68 a kan kowane kliowat zuwa Naira 225 a kan kowane kilowat.
Mataimakin Shugaban Hukumar NERC Musliu Oseni wanda ya bayar da sanarwar ya ce an yi karin ne don a rage nauyin da ke kan Gwamnatin Tarayya saboda faduwar darajar Naira da kuma karin farashi da aka samu a iskar gas.
Sai dai mafi yawan mutanen da suka yi magana da Aminiya sun koka game da yadda aka dora musu nauyin biyan abin da ba su yi amfani da shi ba.
Mazauna Birnin Abuja wadanda suke samun wutar lantarki daga Kamfanin Rararba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) sun koka game da yadda ake samun mutanen da ke zaune a unguwa daya amma sai a iske an sa su a tsari mabambanta da juna.
Wasu mazauna Abuja da aka sanya su a Rukunin A, suna shirin barin wasu unguwanni don komawa wasu, don kauce wa sabon farashin.
Madam Amina Adeola da ke zaune a gida Mai lamba 7B a Rukunin Gidajen Shagari Kwatas a Unguwar Dei-Dei a yankin Bwari ta koka kan yadda Kamfanin AEDC ya dora ta a kan Rukunin A, yayin da sauran abokan zamanta a gidan haya suke rukunin B da C.
“Ba zan iya daukar wannan abin ba. Me ya sa za su sa ni, ni kadai a Rukunin A, bayan ga wadanda muke tare da su a gida daya suna rukunonin B da C?
“Wannan unguwa ce da ba mu samun wutar lantarki sosai. Zan fara zuwa wurinsu in yi musu korafi a ofishinsu na Kubwa, kafin in yi tunanin daukar mataki na gaba.
“Amma dai maganar gaskiya hakan zai iya sa in bar wannan wuri tare da komawa wata unguwar,” in ji ta.
Wata da ke unguwar mai suna Iyabo Ganiyu wacce aka mayar da ita Rukunin A bayan abokan zamanta suna Rukunin C, ta ce tuni ta yi magana da mijinta cewa ya je ya yi wa Kamfanin AEDC korafi.
Shi ma Obas Emmanuel wanda ke zaune a Kubwa ya ce ya gano cewa yana Rukunin A, ne bayan ya sayi katin Naira 3,000 don sawa a mitarsa.
“Da na sayi katin sai na ga an ba ni unit 12, maimakon 40. Hakan ya sa na gane ina Rukunin A, duk da cewa ba na cikin wadanda suke samun wutar lantarki ta awa 20,” in ji shi.
Ya ce daga baya ya gano cewa NERC ta dawo da layinsu a Rukunin B, saboda ba sa samun wutar da ta kamata.
Yakubu Lawal wani abokin huldar Kamfanin AEDC ya ce ya sayi unit 40 a kan Naira dubu 10, alhali a baya da wannan kudi yana samun unit 135.
Ya yi mamakin yadda duk da cewa an mayar da su Rukunin B, amma har yanzu yana biyan kudin wuta na Rukunin A.
Ya yi kira ga Hukumar NERC ta duba matsalarsa don ta nema masa hakkinsa daga Kamfanin AEDC.
Masu amfani da wutar a jihohi sun koka
Eze mai tsara manhaja a kwamfuta da ke zaune a Unguwar Kay Farm a Jihar Legas ya shaida wa Aminiya cewa: “A gaskiya ina samun wutar lantarki sosai a inda nake.
“Sai dai jiya na tashi zan sa katin wutar na Naira dubu daya sai na ga an ba ni unit 4. A yanzu da nake magana ba zan iya amfani da na’urar sanyaya daki ba, sai dai kawai in yi amfani da fanka.
“Sau biyu ina sa katin wutar lantarki daga jiya. Ba na tunanin zan iya jure wannan sabon tsarin biyan kudin wuta da na samu kaina a ciki,” in ji shi.
Wata da ke zaune a yankin Ojodu Abiodun a Legas, ta ce a ranar Alhamis ta sa katin Naira 5,000 sai ta ga unit 22 ne.
Shi ma wani mazaunin yankin ya koka game da yadda ya samu unit 53 a kan Naira 5,000, duk da dai ban bayyana rukunin da yake ba.
Wata da ke Obalande a karkashin Kamfanin Rarraba Lantarki na Eko (EEDC), ta ce lokacin da ta sayi katin mitar wutar lantarkin na Naira 5,000 ta samu unit 20, maimakon 74 da ta saba samu, sai ta nemi bayani kan abin da ya janyo haka.
Manajan Kantin Goodluck Store da ke Surulere mai suna Dubem ya koka cewa karin kudin zai shafi sayen wutar lantarkin da yake amfani da ita.
“A baya ina sayen katin wutar lantarki na Naira dubu 30 wanda yakan yi min tsawon wata biyu. Amma wannan kari abin da za su ba ni ba zai wuce wata daya ba.
“Abin da hakan zai iya haifar da karin kudi a kan kayayyakinmu,” in ji shi.
Ya ce Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko sau biyu suke ba su wutar lantarki a mako.
“Ba mu faye samun wuta a wannan unguwa ba, a lokuta da dama muna samun wutar ta kwana biyu a cikin mako guda.
“Ita ma ta kwana biyun ana bayar da ita na tsawon awa hudu zuwa biyar ne kawai, sauran awannin da ranakun muna amfani ne da janareta,” in ji shi.
Jami’an wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun tabbatar da cewa akwai matsala a wasu yankuna, wadanda a bisa kuskure aka sa su a Rukunin A, inda suka ce an gano su kuma za a mayar musu da kudinsu.
Wani jami’in Kamfanin EEDC, ya ce, “Yanzu haka muna shirin aikewa da sako ga dukkan abokan huldarmu da aka sa a Rukunin A bisa kuskure cewa za mu dawo musu da kudinsu. Muna aiki da kamfanonin sadarwa kuma za mu fita yau, (ranar Juma’ar da ta gabata).
“Mun gano abokan cinikin kuma mun cire su daga tsarinmu kuma za mu tuntube su duka,” in ji jami’in.
Sai dai mai magana da yawun Kamfanin Wutar Lantarki na Ikeja, Kingsley Okotie ya musanta batun da masu amfani da wutar ke yi cewa an yi kuskuren sanya su a Rukunin A, inda ya ce tuni aka warware wannan matsalar tun kafin a fara amfani da sabon kudin wutar.
“A gaskiya ban san wani korafi cewa an yi kuskuren sanya wasu a Rukunin A ba, domin tun farko aka riga an warware wannan matsalar ta yadda kowa yake kan tsarin da ya dace da shi.
“Ina amfani da wannan dama wajen sanar da abokan huldarmu cewa za mu samar musu da wutar da za ta ishe su a wannan lokacin,” in ji shi.
Zai yi wahala a iya biyan karin kudin — Al’ummar Kebbi
Wasu mazauna Rukunin Gidajen Gwamnati na Gesse da sababbin wurare a titin zagaye (Bypass) a Birnin Kebbi sun koka a kan karin kudin wutar da aka yi.
Wasu da suka tattauna da Aminiya sun yi zargin cewa tun kafin wannan kari suke biyan kudin wuta mai yawan gaske, kamar yadda wani Alhaji Abubakar Abbas ya bayyana.
“A kowane wata ina biyan kudin wutar lantarki Naira dubu 60. Wani lokaci kuma dubu 70.
“A yanzu kuma da aka yi wannan kari ba na jin zan iya biyan kudin wutar lantarkin,” in ji shi.
Su ma masu masana’antu da ke Kalgo sun koka cewa ba za su iya biyan sabon karin kudin wutar lantarkin ba “Tuni kasuwancinmu a wurin nan ba ya cikin hayyacinsa saboda matsin tatatlin arziki da aka shiga.
“Ba zan iya tababatrwa cewa da yawa daga cikinmu za su iya biyan kudin wutar lantarkin nan ba,” in ji Sulaiman Babagoro wani da ke da dan karamin kamfanin casar shinkafa a Kalgo.
Abdul’azeez Abdullahi shi ne Mai magana da yawun Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (KAEDCO), da ke bai wa Jihar Kebbi wuta ya bayyana cewa duk wanda yake kan Rukunin A ko kamfani ne ko daidaiku zai biya kudin wuta daidai da tsarin da yake kai.
Abokan hulda ne za su ji a jikinsu —Telolin Kano
Alhaji Abdulhamid Adamu wani tela a Unguwar Badawa a Jihar Kano ya bayyana cewa “Karin kudin wutar da aka yi zai tilasta mu kara kudin aikinmu.
A da da muke dinka riga wacce babu adon komai a jikinta a kan Naira 1,500 zuwa 2,000 biyu a yanzu za mu rika karbar Naira 3,500 zuwa 4,000.
Shi kuwa dinki mai ado da muke karbar Naira 5,000 zuwa 6,000 yanzu zai koma Naira 7,000 zuwa 8,000 ya danganta da irin adon da mutum ya zaba a yi masa.”
Su ma masu yin kankarar a Sharada sun bayyana karin a mastayin abin da ya rikita musu lissafi.
Abubakar Umar ya ce mafi yawansu sun shiga rudani da suka ji labarin karin kudin wutar lantarkin.
Ya bayyana cewa a duk wata yana biyan Naira dubu 500 kafin a yi karin. “Ni da abokan kasuwancina mun shiga rudani yadda za mu yi wa kwastominmu bayanin irin wannan mugun kari na ninki uku.
“A gaskiya za mu dora biyan wannan kudi a kan masu sayen kayanmu,” in ji shi.
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Kamfanin KEDCO, Sani Bala ba ta samu zantawa da shi ba, sai dai wani jami’i a kamfanin wanda ya nemi a boye sunansa ya ce ana iya samun canjin tsarin wutar ma’ana a samu mutum yana wani tsarin ya dawo wani tsarin inda ya ce za a shawo kan wannan lamari.
Mutum miliyan 1.5 ne abin zai shafa — Minista
Da yake magana a kan korafekorafen da ’yan Najeriya ke yi kan karin kudin wutar lantarkin, Ministan Wutar Lantarki Adebayo Adelabu a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a ya ce talaka zai amfana daga karin kudin.
Ya ce bisa lissafin da aka gudanar sama da mutum miliyan 12 ke amfani da wutar lantarki a kasar nan, sai dai karin zai shafi mutum miliyan 1.5, sauran miliyan 10.5 za su ci gaba da morar tallafin na Gwamnatin Tarayya.
Ministan ya ce ko masu masana’antu za su amfana da karin domin za su fi samun sauki a kan kudin da suke kashewa a kan dizal wajen sanyawa a injinansu.
NERC ta ci tarar Kamfanin AEDC Naira miliyan 200
Hukumar NERC ta bakin Mataimakin Shugabanta Oseni ta ce ta ci tarar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) Naira miliyan 200 saboda ya yi kudin goro wajen karin a kan dukkan abokan huldarsa.
Ya ce wannan abin cin amana ne kuma cin tarar kamfanin da aka yi abu ne da zai zama izna ga sauran kamfanonin rarraba wutar lantarkin don kada su maimaita abin da ya Kamfanin AEDC ya yi.
Ya bayyana cewa tarar ta Naira miliyan 200 za ta tafi ne ga Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Karkara.
Ya ce, “Abin da ya janyo karin shi ne wasu kwastomomi sun yi korafin cewa ba su samun wutar awa 20 don haka suka je don a tankwara kamfanonnin sai kuma ga shi an caje su da sabon tsarin.
“Abin da ya faru a Abuja abu ne da ba za a iya kawar da kai ba, Kamfanin AEDC yana ta cewa kuskure ya yi.
To me ya sa ba su yi kuskuren rage wa dukkan kwatomominsu ba?”
Sai dai duk kokarin Aminiya na jin ta bakin Shugabar Sashen Hulda da Jama’a na Kamfanin AEDC, Mimi Angyu ya ci tura kasamncewa ba ta amsa kira ko sakonnin da aka yi ta tura ta wayarta ba.