✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC

ADC na zargin gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da…

Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga  hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini.

Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da kuma kusoshinta daga yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Bolaji Abdullahi ya ce, “muna da sahihan bayanan sirri cewa manufar taron ita ce domin razanawa da tursasa wadannan shugabannin jam’iyar su shirya wa ’yan adawar makarkashiya. Wannan ba siyasa ba ce, tsurku ce.”

Ya ci gaba da cewa, hadafin taron na su shi ne “kawo rudani a jam’iyyarmu, bayyana shugabanninta a matsayin haramtattu da kum kawar da ita daga manufofin da ta sanya a gaba, lura da karuwar yadda jam’iyyar take kara samun farin jini a tsakanin ’yan Najeriya

“Wannan shirin na karkatar da hankalin ciyamomin ADC na jihohi da jami’an gwamnati da ya kamata su mayar da hankali kan warware matsalar tsaron da saurannsu da suka addabi kasa, suke yi, ba komai ba ne face hari ga tsarin dimokuradiyya.

“Daga haka ake fara samun kasa mai tsarin jam’iyya daya—ta hanyar barazaa,” in ji jami’in na ADC.

Ya ci gaba da cewa, “Hadar ADC ta rikita APC kuma yanzu ta bayyana cewa Gwamnatin Tiubu wadda ta rasu goyon  bayan ’yan Najeriya ba za ta iya jure matsin da take ciki a sakamakon wannan hadaka da nagarta ba.

“Amma kuma a maimakon ta gyara kurakurenta sai ta kare da kokarin amfani da tsohuwar dabararta ta kawo rudani a jam’iyyun adawa.”

Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ta ’yan Najeriya ce, wadanda suka gaji da karairayi da yaudara da kuncin rayuwa. Ta ’yan Najeriya ne masu burin dawo da martaba da kyakkyawan fata da kuma adalci a shugabanci.
“Saboda haka ba za mu bar wasu tsirarun mutane masu kama-karya su mayar da kasar nan mai jam’iayya daya ba. Hallo kane a kan kowannenmu ya yaƙi hakan ta yadda ya kamata.”