✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya za ta dawo da ’yan gudun hijira dubu 91 daga Kamaru

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen dawo da ’yan gudun hijira ’yan Najeriya dubu 91 da a yanzu suke zaune a kasar Kamaru. Aikin dawo da…

Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen dawo da ’yan gudun hijira ’yan Najeriya dubu 91 da a yanzu suke zaune a kasar Kamaru. Aikin dawo da ’yan gudun hijirar, wadanda ta’addancin Boko Haram ya kora kuma suke zaune a sansanin kauyen Minaowa, za a fara shi ne a karshen watan Fabrairun nan. Shugaban Kwamitin Kula da Bayar da Taimako da Sake Tsugunnar da ’Yan Gudun Hijira na Kwamitin PCNI, Dokta Sidi-Ali Mohammed ya ce wata hukumar da Gwamnatin Tarayya ta kafa da kasar Kamaru da kuma Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya (UNHCR) sun kammala shirye-shirye don dawo da wadanda aka raba da muhallinsu zuwa kasar nan.

Dokta Muhammad, wanda ya bayyana haka a yayin gudanar da taron wata-wata da ya gudana a ranar 25 ga Janairun bana, ya ce shirin kwaso ’yan gudun hijirar na kan hanya. “A halin yanzu muna kan tantance sansanonin da za a ajiye su. Muna son fara kwaso su a farkon watan Fabrairu, amma dai zuwa karshen watan za a kammala dukan shirye-shiryen fara kwaso su. Mutanen sun kosa su dawo gida Najeriya,” inji shi. Yayin da yake mai da martani game da jita-jitar da ake yadawa cewa ana cin zarafin mata ta hanyar fyade a sansanonin da ke Arewa maso Gabas, ya ce kwamitin PCNI ya sanya matakan tsaro sosai a dukan sansanonin ’yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabas kuma batun kariya ga fyade shi ne babban matakin da ke kan gaba. Ya ce kwamitin na PCNI yana kan tattara bayanan dukan ’yan gudun hijira da ke sansanonin, domin shirya abin da ya shafi abinci da sauran kayan kyautata rayuwarsu, ta yadda za a maida su cikin iyalansu.