✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta kulle wasu gidajen mai saboda ha’inci a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta kulle wasu gidajen mai na kamfanonin Forte Oil da na Dan Oil, a Abuja saboda ma’aikatan gidajen man suna ha’intar mutane ta…

Gwamnatin Tarayya ta kulle wasu gidajen mai na kamfanonin Forte Oil da na Dan Oil, a Abuja saboda ma’aikatan gidajen man suna ha’intar mutane ta hanyar yi musu aringizon kudin mai idan sun zo sayen mai a wurinsu.

Jami’an Awo da Sikeli na Ma’aikatar Kasuwanci ta Tarayya ne a shekaranjiya Laraba suka gudanar da bincike a gidajen mai daban-daban da ke Abuja, ciki har da wadannan gidajen mai biyu na Forte Oil da Dan Oil da ke Unguwar Maitama Abuja, inda suka samu kan famfuna uku da ba su sayar da mai yadda ya dace, suna yin kwange ko aringizo ga masu sayen mai.

Mukaddashin Darakta na ma’aikatar wanda ya jagoranci binciken, Injiniya Muhammad Sada Sidi ya ce sun bankado cewa wasu fanfunan sayar da fetur a gidan mai na Forte Oil suna ha’inci ta yadda duk lita 40 da aka saya suna yin kwangen lita daya daga ciki. Ya ce  sakamakon wannan ha’inci, a duk lita 33,000 da gidan man ya sayar, suna cutar mutane kimanin Naira dubu 194.

Haka kuma an gano irin wannan almundahana a gidan mai na Dan Oil da ke kan Titin Airport a Abuja. A wannan gidan mai ne jami’an binciken suka gano yadda ake cutar duk wanda ya zo sayen mai, inda a duk lita 20 da aka saya, ana cutar mai saye rabin lita.

Injiniya Sidi ya ce, a wadannan gidajen mai na Forte Oil da Dan Oil da aka gano suna ha’inci, nan take suka soke lasisinsu kuma ba za a mai da masu ba har sai lokacin da suka gyara aikinsu zuwa daidai da yadda hukuma ta kayyade.

Ya kara da cewa wannan mataki na bincike da suke gudanarwa, suna yi ne da nufin kare al’umma daga cutarwa. Aikinsu ne su tabbatar da cewa ba a yi wa mai saye kwange ko aringizo ba.