Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana damuwarsa kan zanga-zangar da ake yi a sassan jihar sakamakon karancin kudi.
Sai dai gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bukaci masu zanga-zangar da su kwantar da hankalinsu har zuwa lokacin da Kotun Koli za ta zartar da hukunci.
- Canjin kudi: Buhari ya talauta mu baki daya —Kwankwaso
- Ba za mu daina amfani da tsoffin kudi ba —El-Rufai ga Buhari
Aminiya ta ruwaito yadda tarzoma ta fantsama a yankunan Mile 12, Ojota, Ketu, Agege, Ikotun, Epe, da dai sauransu a birnin na Ikko.
An baza ‘yan sandan kwantar da tarzoma a wurare daban-daban yayin da Kwamishinan ‘Yan sanda, Idowu Owohunwa ke zagayawa wuraren da aka samu tashin hankali a jihar.
Da yake magana game da lamarin, Sanwo-Olu ta bakin Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Gbenga Omotoso, ya bayyana “damuwa sosai”.
A cewar sanarwar, “masu zanga-zangar sun fusata ne kan sauya fasalin takardun Naira da kuma karancin kudin da ya jawo wa al’ummarmu wahala da rudani.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi imanin cewa babu bukatar yin tashin hankali saboda Kotun Koli za ta bayyana matsayarta a ranar 22 ga watan Fabrairu.
“Jihar Legas ta shiga batun shari’ar – duk don maslahar jama’armu – bisa imanin cewa Kotun Koli na da ikon yanke hukunci a kan lamarin.
“Karancin mai ana samun sauki bayan wasu matakai da gwamnati ta dauka.
“Gwamnati ta yaba wa ‘yan Legas da suka fahimce ta, duk da radadin da matakan Gwamnatin Tarayya suka haifar.
“Ya kamata mutane su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda ta hanyar gujewa duk wani nau’in tunzura jama’a daga masu aikata barna za su yi.
“Gwamna yana aiki tare da takwarorinsa don ganin cewa wannan wahalhalun ba su ci gaba da faruwa ba.”