✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta daina biyan tallafin kuɗin aikin hajji

Yanzu haka dai an fara raɗe-raɗin cewar kuɗin aikin Hajjim 2025 zai iya kai wa miliyan 10.

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta ci gaba da biyan tallafin kuɗin aikin hajji ba.

A baya, gwamnati tana taimakawa ta hanyar rage kuɗin canjin dala, wanda ake bai wa maniyyata damar sayan dala a farashi mai rahusa daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Amma a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce ba za a bai wa maniyyata tallafin ba a 2025.

Wannan na nufin idan farashin canjin Naira ya tafi a kan Naira 1,650 kan kowace Dala, kowane mutum zai biya kusan Naira miliyan 10 domin zuwa aikin hajji.

An yi hasashen cewa kuɗin aikin hajjin 2024 na iya kamawa kan Dala 6,000.

Duk da cewa NAHCON ba ta bayyana adadin kuɗin aikin hajji na 2025 ba, hukumomin kula da jin daɗin alhazai na jihohi sun fara neman maniyyata su biya Naira miliyan 8.5 a matsayin kuɗin ajiyar farko kafin a sanar da farashin a hukumance.

Wannan sanarwar ta fito ne bayan wani taron tattaunawa tsakanin NAHCON da masu shirya tafiye-tafiye masu zaman kansu (PTOs).

A yayin taron, Kwamishinan ayyukan NAHCON, Prince Anofi Olanrewaju Elegushi, ya bayyana sabbin sauye-sauye da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta samar.

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne Saudiyya ta rage yawan kamfanonin masu zaman kansu daga 20 zuwa 10, kuma kowane kamfani dole ne ya yi rijistar aƙalla mahajjata 2,000 kafin a ba shi izinin samun bizar hajji.