Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu.
Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
- Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda
- Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano
Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa.
Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida ke yi ne ke ƙara kawo barazana ga tsaron ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar soji da ke Abuja a yayin a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin kafafen yaɗa labarai.
Ministan wanda babban daraktan kafar Muryar Nijeriya, Jibril Ndace ya wakilta, ya ce gwamnatinsu na ƙoƙari wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, ta hanyar samar wa jami’an tsaro kayan aiki, horo, da tattara bayanan sirri.