Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin, 3 ga watan Mayun 2021, a matsayin ranar hutu domin bikin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya ta wannan shekarar.
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Rauf Adesoji Aregbesola ne ya ayyana ranar a madadin gwamnatin tarayya a wata takarda da babban sakatare a ma’aikatar, Shuaib Belgore, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
- Yadda aka yi wa Fulani kisan gilla a Anambra
- Geidam: Gwamnan Yobe ya ziyaraci Sarkin Kano
- Yadda Boko Haram ta raba kyautar kudade a Geidam
Ministan ya taya daukacin ma’aikatan Najeriya murnar sake ganin zagayowar wannan rana.
Tsohon gwamnan na jihar Osun kuma yaba wa ma’aikata kan hakuri da fahimta da ma goyan-bayan da suke bai wa tsare-tsaren gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kokarinta ciyar da kasar gaba ta fuskar bunkasa tattalin arziki.
Kazalika, Aregbesola ya yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su ci gaba da sadaukarwa da nuna kishin kasa a dukkan al’amuransu.
Ya ce, “Gwamnati na daukar dukkan wasu matakai da suka dace na ganin an kawo karshen matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan.
“Muna kira da Kungiyoyin ma’aikata da masu kishin kasa da su yi iya bakin kokarinsu, su bayar da tasu gudunmawar wurin kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta,” a cewarsa.