Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewar ta gamsu da matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da matsalolin tsaro a ƙasar nan.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Kano.
- Matatar Dangote za ta iya sayar wa ’yan kasuwa fetur — NNPCL
- Mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki
Bichi, ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, da sauran ƙungiyoyin tsaro a ofishinsa.
Wannan na zuwa ne bayan ziyarar tattaunawa kan illar da tsattsauran ra’ayi ke kawowa ga zamantakewa da tattalin arziƙin Kano, da kuma hanyoyin kawo karshen lamarin.
Kazalika, ya ce Gwamnatin Kano tuni ta fara aiwatar da tsare-tsaren da ta ke da yaƙinin za su yaƙi matsalar lamarin, wacce yawanci talauci da rashn ilimi ke jawowa.
“Muna sane da cewa talauci na taka muhimmiyar rawa wajen aikata miyagun laifuka, don haka ne daga shigowarmu gwamnati muka ƙirƙiri ma’aikatar jin-ƙai da yaƙi da talauci.
“Ba wai zuwa za mu yi da wasu tsare-tsare sabbi a ma’aikatar ba, a’a, za mu yi amfani ne da waɗanda ƙasashen duniya irin su Brazil da China suka yi amfani da su suka cire miliyoyin al’ummarsu daga talauci a shekaru 20 kacal.”
A nata ɓangaren, Hajiya Mairo Abbas, wakiliyar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, ta ce tattaunawar na da matuƙar muhimmanci, domin harkar tsaron Kano al’ amari ne da shafi ƙasa baki ɗaya.
“Mun zo ne domin neman goyon baya da haɗin gwiwar Gwamnatin Kano don ƙara bunƙasa ayyaukan da muke yi na bunƙasa tsaro tare da haɗin guiwar ƙungiyoyi da ita kanta gwamnatin domin waɗannan tsare-tsaren su ɗore.
“Muna so kuma mu sanar da gwamnatin cewa mun kafa wata ƙungiya domin haɗa guiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da muke fatan yakar tashe-tashen hankula da tsatsauran ra’ayi ne ke kawo su a Kano, domin yaƙar dabi’ar. Muna ganin hakan zai taimaka matuƙa wajen ci gaban jihar.”
A nata jawabin mataimakiyar babbar daraktar ƙungiyar Action Aid l, Hajiya Suwaiba Dan Kabo, ta ce sun kai ziyarar ne, saboda muhimmancin da Jihar Kano ke da shi ga tsaron Najeriya.
“Zanga-zangar baya-bayan nan a aka gudanar a Kano, ta nuna ƙarara akwai buƙatar miƙewa tsaye wajen yaƙar tashe-tashen hankula, musamman domin kare yaranmu masu tasowa. Wannan babban ƙalubale ne ga masu ruwa da tsaki, domin ɗaukar matakan da suka dace a gwamnatance.
“Wannnan ne ya sanya ƙungiyarmu tun fiye da shekara ɗaya da ta wuce ta fara ƙoƙarin ƙarfafa al’umma su yaƙi wannan mummunar akidar ta tsattsauran ra’ayi.
“Mun fara da ƙananan hukumomin Gwale, Nassarawa, Bichi, Gwarzo, Bebeji da Tudun Wada,” in ji ta.
Ta ƙada da cewar “Haka ma a unguwannin irin su, Gwale, Dorayi, Nassarawa, Tagarji-Tudun Murtala, Bichi, Danzabuwa, Gwarzo, Getso, Bebeji, Kofa, Yaryasa, da Tudun Wada.
“Kazalika, mun kashe kimanin Naira miliyan 5 domin horaswa da kuma samar wa matasa da mata sana’o’i, inda muka raba musu injin sarrafa shinkafa, man ƙuli, da kuma ɗinki.”