Ministan Bunƙasa Harkokin Ƙarafa, Shuaibu Abubakar Audu, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na samun ci gaba wajen farfaɗo da tsohon kamfanin ƙarafa na Ajaokuta da ke Jihar Kogi.
Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudanar da manyan jiga-jigan jam’iyyar APC na Jihar Kogi a garinsu Ogbonicha da ke Ƙaramar Hukumar Ofu.
- Mutum 9 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa
- Magidanci ya shiga hannu kan kashe matarsa mai juna biyu da duka
Ministan, ya ce Gwamnatin Tarayya ta riga ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin da za su samar da kayan aikinkamfanin.
Ya ƙara da cewa gwamnati na ƙara neman masu saka hannun jari daga ƙasar China domin su zuba jari a kamfanin.
“Muna yin aiki babba. Mun fara tafiya, kuma muna da tabbacin cewa za mu dawo da aikin Ajaokuta cikin sauri,” in ji Audu.
Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda tsare-tsarensa na gyara da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan ta hanyar inganta harkar sarrafa ƙarafa.
Ya ce Shugaban Ƙasa na ƙoƙarin warware matsalolin da ke addabar ƙasar nan da kuma inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
Audu, ya ce shirin “Sabunta Fata” da Shugaban Ƙasa ke jagoranta ya riga ya fara haifar da ɗa mai ido.
Ya bayyana saukar farashin wasu kayan abinci a matsayin misali.
Haka kuma ya bayyana cewa kuɗin da jihohi ke samu daga Asusun Gwamnatin Tarayya (FAAC) sun ƙaru, lamarin da ya taimaka wa Jihar Kogi.
A nasa jawabin, Sakataren APC na Jihar Kogi, Joshua Onoja, ya yaba wa Ministan bisa shirya taron, sannan ya tabbatar da cikakken goyon bayan jam’iyyar wajen sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar daga sassa daban-daban na Jihar Kogi, ciki har da shugabannin ƙananan hukumomi, ’yan majalisa na yanzu da na baya, ƙungioyi da sauransu.