✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Soji ta karya farashin shinkafa a Nijar

Duk dan kasuwar da bai kiyaye sabon matakin da muka ɗauka ba za mu ɗora shi a kan saiti.

Gwamnati Soji mai mulki a Jamhuriyyar Nijar, ta karya farashin shinkafa da ta yi tashin gwauron zabi a watanni baya bayan nan.

Tun dai lokacin da Ƙungiyar ECOWAS ta sanya wa Nijar takunkumin karayar tattalin arziki bayan juyin mulki kusan watanni bakwai da suka gabata, farashin shinkafa ya yi tashin gwauron zabo.

Bayanai sun ce tun a wancan lokacin farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 ya tashi daga jikka 11 na CFA zuwa jikka 15 har zuwa 18 a wasu yankunan kasar.

Sai dai a yanzu Gwamnatin Sojin da ta kifar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, ta ƙuduri cewa za a riƙa sayar da buhun shinkafar mai nauyin kilo 25 kan Jika 13 na CFA a birnin Yammai.

Haka kuma, gwamnatin ta ƙayyade farashin buhun shinkafar mai nauyin kilo 25 kan Jika 13 da dala 135 a Dosso, Jika 13 da dala 165 a Tahoua, Jika 13 da dala 185 a Maradi, Jika 14 daidai na CFA a Damagaram, Jika 14 da dala 75 a Diffa, Jika 14 da dala 25 a Agadez sai kuma jika 13 da dala 130 na CFA a Tillabery.

Malam Ayuba Djimrao, babban mai ba da shawara ga Ministan Kasuwanci na kasar, ya bayyana dalilin karya farashin shinkafar a daidai wannan lokaci.

A cewarsa, “mun duba mun ga duk makwabtan da ke kewaye da mu, babu inda farashin shinkafar yake jikka 13 na CFA.

“Saboda haka muka nemi haɗin kan dukkanin masu ruwa da tsaki domin yadda za a yi wa wannan tufkar hanci.

Malam Djimrao ya ce sun ɗauki wannan ƙuduri ne domin su ceci al’umma da kuma ƙasa baki ɗaya la’akari da halin da ake ciki musamman yadda watan Azumin Ramadana ya tunkaro.

Ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai taimaka wa al’umma su gudanar da ibadar Azumin Ramadana cikin sauƙi.

Ya ƙara da cewa, duk da yake akwai takunkumi da aka kakaba wa ƙasar, amma hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba, “kuma duk dan kasuwar da bai kiyaye wannan sabon mataki da muka ɗauka ba, za mu mayar da shi kan saiti.”

Tuni dai kungiyar manyan ’yan kasuwa masu shigo da haja daga ƙetare ta yi amanna tare da ba haɗin kai dangane da wannan sabon mataki

A cewar shugaban kungiyar ’yan kasuwar, Ila Hatimi Mai Aya, “tunda har gwamnati ta sakankance cewa ta ɗauki wannan mataki bisa lissafin yadda ’yan kasuwa za su fita, to mu abin da za mu ce wannan abu ne mai kyau.

“Kuma abin dubawa shi ne yadda watan Azumin Ramadana ya tunkaro, kuma ga wannan mataki da gwamanti ta ɗauka, ko babu komai duk wanda ya tallafa mabukata a irin wannan lokaci yana da sakamakon na alheri a wurin Ubangiji.”

Ita ma ƙungiyar da ke kare haƙƙin masu sayen haja a Nijar ta bakin shugabanta, Malam Mamman Nuri, ta yaba da wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka.

Da yake bayyana gamsuwarsa kan sabon mataki, Malam Nuri ya yi kira ga gwamnati da ta miƙe tsaye don ganin an kiyaye umarninta sau da kafa.

Ya bayyana cewa a matsayinsu na kungiyar kare haƙƙin masu sayen haja, za su baza idanu tare da miƙa wa gwamnati rahoton duk wata cibiyar kasuwanci da farashin shinkafar ya sha banban da yadda gwamnatin ta ƙayyade.