Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta ba da gudunmawar kayan abinci da gidan sauro ga Malam Lawwali Maishinkafa Illela, wanda matarsa Malama Shafa’atu ta haifa wa ’yan hudu a ranar Litinin din da ta gabata a karamar Hukumar Illela da ke jihar. Mai jegon da jariran wadanda duka mata ne suna nan cikin koshin lafiya.
Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Jin Dadin Jama’a, Alhaji Sirajo Gatawa ne ya mika kayan ga iyayen ’yan hudun a gidansu da ke garin Illela, inda ya bayyana cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya umarce shi ya bayar da wannan tallafi bayan sanar da shi da aka yi game da haihuwar.
Ya ce Gwamna Tambuwal yana bakin kokarinsa wajen kula da jin dadin jama’a, domin duk lokacin da aka nemi ya ba da tallafi ga wanda ke da bukata yana badawa. Sai ya bayyana sakon Gwamnan na taya iyayen murnar samun wannan baiwa da Allah Ya yi musu tare da addu’ar samun lafiya ga uwar da abin takalifi ga mahaifin.
Kwamshina Gatawa ya mika tallafin kayan abinci da tufafin yara da na mahaifiyarsu da gadajen jarirai da katifu masu gidan sauro da madararar jarirai da sauransu ga iyalan.
Sai ya mika wa mahaifin Naira dubu 500 daga Gwamna Tambuwal a matsayin tasa gudunmuwa.
Shugaban karamar Hukumar Illela ya gode wa Gwamnan kan tallafin da aka ba iyalan,kuma ya hada matar da jami’an kiwon lafiya don ba su shawarwari kan yadda za a kula da renonsu.
Malam Lawwali da matarsa sun nuna farin cikinsu tare da godiya ga Gwamna Tambuwal kan tallafin da ya kai musu ganin wannan haihuwar sabuwa ce a wurinsu kuma ba wani karfi suke da shi ba.
Mahaifin ya yi farin ciki da samun ’ya’yan da fatan Allah Ya yi samu albarka kuma ya ce ba zai taba gajiyawa wajen yi musu hidima ba har karshen rayuwarsa.