Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta yi zaman tattaunawa da wasu bata-gari da kungiyoyin matsafa da na asiri a jihar domin wanzar da zaman lafiya da kawo karshen ayyukansu.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu da Yawon Bude Ido na Jihar Dokta Wasiu Olatunbosun ya bayyana haka ranar Alhamis, bayan wata ganawar sirri da ya yi da wakilan kungiyoyin.
- N-Power: CBN zai ba wa matasa 300,000 da aka yaye rance
- Shugabannin Hausawa sun fara gyara wa fitsararru zama
Daga cikin wadanda aka yi ganawar da su a birnin Badun har da kungiyar OPC da ta ‘yan sintiri ta Najeriya (Vigilante Group of Nigeria) da sauransu.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar, da hadin gwiwar dukkanin kungiyoyin matasa masu amfani da makamai, ta kuduri aniyar kawo karshen tashe-tashen hankalin da ake yi da zubar da jini a tsakanin matasa ‘yan unguwa da kungiyoyin matsafa.
Ayyukan kungiyoyin asiri da fadace-fadace a tsakanin matasa a Jihar sun yi kaurin suna, lamarin da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma masu tarin yawa.