Gwamnati da mahukunta a Jamhuriyyar Nijar sun soma shirye-shiryen dakile matsalar yada bidiyon tsiraici a kafafen sada zumunta musamman a tsakanin matasa mata da maza.
Wata ‘yar Majalisar Tarayyar kasar daga bangaren masu rinjaye a kasar, ta shawarci takwarorinta ‘yan majalisa da ma hukumomi a kan bukatar nazarin hanyoyin warware sarkakiyar da ke tattare da dokokin kasar game da batun mu’amular mutane masu jinsi daya.
’Yar majalisar, Nana Jubi Harouna Maty, ta bada wannan shawarar ce bayan da a farkon watan nan na Oktoba mahukunta suka kama wasu ‘yan mata da ake yi wa kallon ‘yan madigo yayin da hukumomin shari’a ke cewa laifin yada bidiyon tsiraici a kafafen sada zumunta ne mafarin cafke su.
Hanyoyin da matasan ke bi wajen amfani da kafafen sada zumunta wani abu ne da tun dadewa shugabanin addinai ke jan hankulan iyaye akansu.
Tun a washegarin bayyanar wani bidiyon tsiraicin da ya karade kafafen sada zumunta ne jama’a daga sassan Nijar suka tuntubi ‘yar Majalisar Nana Jubi akan wannan al’amari da ya saba wa tsarin zamantakewar al’ummar Nijar kamar yadda ta bayyana a taron manema labaran da ta kira.
Muryar Amurka ta ruwaito Nana Jubi tana cewa, abun da ya faru a Maradi, abun ta da hankali ne saboda akasarin ’yan Nijar, masu bin addini ne yadda ya kamata.
Girman damuwar da ake ta nunawa bayan faruwar wannan al’amari ya sa ‘yar majalisar yanke shawarar gabatar da korafin ‘yan kasa a zauren majalisar don ganin an samar da dokar kare al’umma daga miyagun ayyukan.
Bayanai sun ce da alamu idan masu bakin fada a ji ba su yi wani abu a kai ba, abin na iya samun gindin zama a sahun al’ummar kasar.
Hanyoyin da matasan ke bi wajen amfani da kafafen sada zumunta wani abu ne da tun da dadewa shugabanin addinai ke jan hankulan iyaye akansu.
A hirar ta da Muryar Amurka, Malama Sakina Maman, daya daga cikin masu gabatar da wa’azin addinin Islama, ta ce duk wasu mata biyu ko maza biyu, ko mace ta ce ita na miji ne ko namiji ya ce shi mace ce, to lalle su yi hankali domin Allah Zai hallaka su kamar yadda ya yi wa wadanda suka zo kafin mu.
Haka shi ma Rabaran Sabo Batchiri na Majami’ar Assemblee de Dieu, ya bayyana cewa wajibi ne a ci gaba da tunatarwa akan nauyin da ya rataya a wuyan shugabanni .
A farkon watan nan na Oktoba ne hukumomin shari’a suka kama wasu ‘yan mata 13 a Maradi wadanda da farko rahotanni suka ce ‘yan madigo ne da dubunsu ta cika.
An kama matan ne bayan bayyanar wani bidiyon da suka nada sai dai a washegari alkali mai tuhuma, ya ce da laifin yada bidiyon tsiraici ne ya kama su a maimakon laifin aikata mu’amula irinta masu jinsi daya da ake ta yayatawa, lamarin da ya sa wasu ‘yan kasa ke ganin akwai bukatar warware wannan kulli.