Kimanin ma’aikata 374 ne Gwamnatin Neja ta kora daga aiki, yayin da wasu 380 kuma ta yi musu ritayar dole saboda karya dokokin aiki.
Gwamnatin ta kuma zargesu da yin karya a shekarun haihuwarsu da kuma shekarun da suka fara aiki.
- Da dumi-dumi: Sanatan Zamfara ta tsakiya ya fice daga PDP
- An kara dage wa’adin hade layin waya da lambar NIN
Kazalika, Gwamnatin ta yi wa wasu ma’aikatan kimanin 6,835 karin girma zuwa matsayi daban-daban.
Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar, Alhaji Yusuf Shehu Galadimawa ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Minna ranar Talata.
A cewarsa, “Hukumarmu a tsaye take wajen tabbatar da da’a a kowanne mataki na aikin gwamnati. Hakan ne ya sa muka bankado ma’aikata 46 da suka karya dokoin aikin, kuma bayan zuzzurfan bincike muka sallamesu.
“Daga cikinsu, har da wani likita, sai ma’aikatan Hukumar Fansho 31, akantoci guda biyar, ma’aikatan lafiya biyu sai na fasahar sadarwa guda hudu.
“Kazalika, mun yi wa mutum 380 ritayar dole saboda samunsu da hannu dumu-dumu a badakalar canza shekarun haihuwa da na shekarar daukar aiki,” inji shi.
Shugaban ya kuma ce akalla mutum 328 ne aka kora daga aiki bayan an gano takardun karatunsu na bogi ne sannan makarantun da suka yi ikirarin gamawa sun nesanta kansu da su.
Jihar ta Neja dai wacce take da ma’aikata kusan 24,000, ta ce ta dauki matasa 1,133 domin cike guraben da aka samu a ma’aikatu, bangarori da hukumomin gwamnati, musamman a bangarori masu muhimmanci irin na lafiya da ilimi da kashe gobara da dai sauransu.