Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin murnar cikar Najeriya shekara 60 da samun ‘yanci.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.
- Najeriya: Buhari ya kaddamar da tambarin cika shekara 60
- Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 a mako mai zuwa
Ya taya daukacin al’ummar kasar murnar zagayowar ranar samun ‘yancin yayin da ya tunatar da jajircewar da Gwamnati ke y i wajen inganta jin dadin al’umma da bunkasa tattalin arziki.
Ministan wanda shi ne tsohon Gwamnan jihar Osun, ya ce cika shekaru 60 da samun ‘yanci lamari mai muhimmanci sa yana kara tuni a kan yadda annobar coronavirus ta sanya dole a takaita shagulgulan da za a yi.