A gobe Asabar, 1 ga watan Oktoba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ’yan Najeriya jawabi dangane da bikin cikar kasar shekaru 62 da samun ’yanci.
Mai magana da yawun Shugaban Kasar, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan.
Sanarwar ta ce Shugaban zai jawabin ne wanda za a haska kai tsaye ta Gidan Talibijin na kasa (NTA) da kuma Gidan Rediyon Najeriya.
Adesina ya bayyana cewa, Buhari zai yi jawabin ne da misalin karfe 7.00 na safe wanda hakan na daya daga cikin sha’anin da za a yi na munar cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Adesina ya ce daga na shugaban zai garzaya Dandalin Eagle wurin taron murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan inda zai kalli faretin jami’an tsaro da sauran shagulgula da za a fara da misalin karfe 10.00 na safe.
“Ana umartar gidajen talabijin da rediyo da sauran kafofin labarai na latironi da su jono jawabin daga gidan talabijin na NTA da kuma Rediyo Najeriya,” a cewar sanarwar.
Tun daga farkon makon nan aka ga sojojin Najeriya na shirye-shiryen bikin na ranar Asabar, inda jiragen soja za su dinga wasa a sama da kuma faretin girmamawa.