Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya samar da shiri na musamman domin rage wa talakawan jiharsa radadin matsin da rashin mai da karancin kudi suka haifar a kasa.
Ya ce shirin ya kunshi raba tallafin kudi ga mata da masu karbar fansho da kananan manoma da ‘yan kasuwa da sauran marasa galihu a jihar hadi da jigilar dalibai da ma’aikata zuwa wajen aiki kyauta.
- Kansiloli sun tsige Shugaban Karamar Hukuma a Kano
- An shiga rudani kan ‘sauya shekar’ Mataimakin Gwamnan Sakkwato
A cewar Gwamnan, shirin ba da tallafin zai gudana ne karkashin kulawar Shirin Zuba Jari na Jihar Kwara (KWASSIP) don tabbatar da komai ya gudana cikin nasara.
“Gwamnan ya bai wa KWASSIP umarnin samar da tsari dangane da yadda za a aiwatar da shirin don rage wa ‘yan jihar radadi,” kamar yadda Sakataren Yada Labarai ga Gwamnan, Rafiu Ajakaye ya bayyana a ranar Alhamis.
Ya ce “Gwamnan ya sake ba da umarnin tura motocin safa zuwa wasu hanyoyi don jigilar dalibai da ma’aikatan manyan makarantu kyauta sakamakon karancin man da ake fuskanta.”
Gwamna AbdulRazaq ya ce shirin jigilar dalibai kyauta zai fara aiki ne ranar Litinin, 13 ga 2023 idan Allah Ya kai mu.