Gwamnatin Jihar Katsina ta karyata labarin da ke cewa an sako daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara da aka yi garkuwa da su.
Sakataren Gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ya ce babu gaskiya a labarin sako daliban da aka yi garkuwa da su a ranar Juma’a da dare amma ana sa ran sako yaran nan ba da dadewa ba.
- Boko Haram ta saki bidiyon Daliban Kankara da ta yi garkuwa da su
- An gano Daliban Kankara a dajin Zamfara
Tun da farko kafar watsa labarai ta Arise TV ce ta sanar da ceto yaran, kamar yadda ita ma Mai ba wa Shugaba Buhari Shawara kan Harkokin ’Yan Najeriya Mazauna Ketare, Abike Dabiri-Erewa ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an sako yara 333.
Boko Haram ta saki bidiyon Daliban Kankara
Sai dai wani sabon bidiyo da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar ta Alhamis ya nuna daliban na GSSS Kankara a hannunta.
Bidiyon ya nuna yaran a cikin daji, inda daya daga cikinsu ya yi jawabi a madadinsu yana neman a cece su tare da zayyano bukatun kungiyar.
“Muna kira ga gwamnati da ta rushe duk wani rukunin masu aikin sa-kai na kato da gora, a rufe kowace irin makaranta sai dai ta Islamiyya.
“A mayar da dukkan sojojin da aka turo nan saboda babu abin da za su iya yi musu wallahi. Jiragen nan ma a daina turowa. A taimaka mana daga halin da muke ciki,” inji dalibin.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta daidaita da masu garkuwar, tare da gargadin kada ta yi amfani da karfin soji wajen kubutar da su.
Daga bayansa an hango wasu daga cikin daliban su 10, kowannensu jikinsa ya yi busu-busu da kura.
Daga karshe kungiyar ta nuna sauran daliban a matsayin shaida cewa suna nan a hannunta.
Daliban dai sun rika yin kuka suna kira ga gwamnati kan ta taimaka ta duba halin da suke ciki domin ta kubutar da su.
Takaddar bidiyon Boko Haram na farko
Bidiyo ya fito ne washegarin ran da Gwamnatin Katsina da Rundunar Tsaro ta Najeriya suka karyata ikirarin kungiyar na sace da daliban.
Da farko, Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a cikin wani sakon sauti ya ce mayakan kungiyarsa ne suka dauke daliban.
Amma Rundunar Tsaro, ta bakin kakakinta, Manjo Janar, John Enenche ta ce ikirarin da na Shekau farfaganda ce kawai.
Enenche ya ce rundunar ta aiki don ceto daliban cikin aminci.
A nashi bangaren, Gwamnan Katsina Aminun Masari ya ce a iya saninsu masu garkuwa da mutane ne suka dauke yaran.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.
Ya kara da cewa an gano yaran suna ajiye ne a ‘dajin Zamfara’, ana kuma tattaunawa da masu garkuwar kan sako daliban.