✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano za ta kafa dakarun yaki da muggan kwayoyi

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin kafa kwamitin dakarun lura da magunguna don taimakawa Hukumar Yaki da Muggan Kwayoyi ta NDLEA yaki da muggan kwayoyi…

Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin kafa kwamitin dakarun lura da magunguna don taimakawa Hukumar Yaki da Muggan Kwayoyi ta NDLEA yaki da muggan kwayoyi a jihar.
Shugaban Hukumar Karbar Korafi da Yaki  da Cin Hanci da Rashawa, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, shi ne ya bayyana haka yayin da ya karbi tawagar Kwamandan Hukumar NDLEA na jihar, Hamza Umar a ofishinsa.
Rimin-Gado ya ce dakarun za su yi aiki tare da jami’an Hukumar NDLEA su yaki ta’ammuli da muggan kwayoyi a tsakanin matasan jihar.
Ya ce gwamnati ta dauki matakin don tallafa wa kokarin gwamnatin tarayya na yaki ga muggan kwayoyi a kasa baki daya.