✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta ware N800m domin koya wa mata sana’o’i

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira miliyan 800 domin magance talauci da rashin aikin yi a tsakanin mata da matasan jihar. Kwamishinar Harkokin Mata da…

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira miliyan 800 domin magance talauci da rashin aikin yi a tsakanin mata da matasan jihar.

Kwamishinar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a ta Jihar, Zahra’u Muhammad Umar, ita ce ta bayyana hakan yayin da take kare kasafin kudin ma’aikatarta na 2022 a gaban majalisar dokokin jihar.

Ta shaida wa majalisar cewa an ware kudaden ne domin magance matsalar talauci da rashin sana’o’in dogaro da kai da ke addabar jama’ar jihar.

Kwamishinar ta ce gwamnatin jihar ta bayar da muhimmanci ga horar da mata da koya musu sana’o’in dogaro da kai a shekarar 2022 karkashin shirinta na koyar da sana’o’in dogaro da kai.

A cewarta, gwamnatin ta bullo da tsare-tsaren ne da nufin farfado da sana’anta kayayyakin amfanin cikin gida, tatsar man gyada da tunkuza da sauranso domin dogaro da kai daga cikin jihar.

Ta bayyana wa majalisar cewa an fara aikin gyaran cibiyar sauya dabi’un masu shaye-shaye da ke Kiru ta yadda za ta iya daukar maza da mata masu yawan gaske domin su amfani al’umma.