Gwamnatin Kano ta ce ta yi mamaki da ganin yadda aka wayi gari wannan Juma’ar jami’an tsaron sun mamaye Fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Bayanai sun nuna cewa a yau ɗin ne aka tsara Sarki Sanusi II zai yi wa ɗaya daga cikin masu riƙe da sarauta mafi girma a masarautar, Wamban Kano Mannir Sanusi, rakiya zuwa Bichi domin kama aiki a matsayin hakimin ƙaramar hukumar.
- Kashi 70 na ’yan Najeriya da aka bai wa cin hanci a shekarar 2023 sun ƙi karɓa — ICPC
- Kyaftin ɗin Ipswich ya tayar da ƙura kan rashin ɗaura ƙyallen ’yan maɗigo
Sai dai jami’an tsaro sun tare ƙofar fita daga masarautar da duk wata hanya da za ta sada mutum da masarautar.
Da yake martani a cikin wata hirarsa da Gidan Rediyon Freedom, Sakataren Gwamnatin Kano Abdullahi Baffa Bichi ya ce, “abin da ya ba mu mamaki shi ne, babu wani abu na fargaba ko tashin hankali a Jihar Kano.
“Wasu tsirarun mutane ne kawai ke so su tayar da zaune a tsaye a Kano waɗanda ke samun goyon baya daga Abuja.
“Sarki ya gayyace mu cewa zai raka hakiminsa ƙasarsa sai muka tashi da jami’an tsaro suna cewa ba za a je ba. Da muka tambaye su sai suka ce umarni aka ba su daga sama.”
Sai dai Sakataren Gwamnatin ya ce suna jiran hukuncin da sarkin zai yanke game da batun.
“Duk lokacin da mai martaba ya shirya za mu yi tururuwa mu raka hakimin Bichi,” in ji shi.
Mu ci gaba da haƙuri — Sarki Sanusi II
A yayin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma’a, Sarkin ya buƙaci mazauna Kano da su yi haƙuri kuma su kwantar da hankalinsu.
“Abubuwan da muke gani, akwai mutane da babu abin da suke nufi da Kano illa su kawo abin da zai haifar da zubar da jini,” in ji shi.
“A cikin ’yan watannin baya, wajen kashi shida ko bakwai ana jarrabawa, ana so mutane su fusata su ɗauki doka a hannunsu.
“Jama’a kada a faɗa wannan tarkon. Duk mutumin da ya kawo fitina a Kano, zuwa zai yi ya tafi, dukiyarmu za a ƙona. A daure a yi haƙuri, haƙuri ba tsoro ba ne, a yi addu’a.”
Wata shida ke nan da rikicin kujerar Sarkin Kano ta ki ci ta ƙi cinyewa tun bayan da gwmanatin jihar ta dawo da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16, bayan ta soke dokar masarautu shida a jihar, wadda ta naɗa Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na 15.
Tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, wadda ba ta ga-maciji da Gwmanati mai ci ta Abba Kabir Yusuf ce ta tsige Sanusi a matsayin Sarki na 14, ta naɗa Aminu Bayero a kan kujerar.