✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure

Shugaban hukumar ya ce ana yin wasu ɗabi'u marasa kyau a lokacin 'ƙauyawa day'.

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Kauyawa Day’ gaba ɗaya.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar.

Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu.

“Daga yanzu, duk wanda ya shirya wani taro da sunan Kauyawa ko Villagers Day, ya karya doka,” in ji El-Mustapha.

Sabuwar dokar ta bai wa hukumar ikon sanya ido da kula da dukkanin cibiyoyin taro da ayyukan DJ a jihar.

Saboda haka ne aka dakatar da dukkanin cibiyoyin taro har zuwa wani lokaci.

An ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga wasu ƙungiyoyin addini da na al’adu kan yadda ake gudanar da bikin Ƙauyawa Day.

Galibin waɗannan bukukuwa matasa da ’yan mata ne ke shirya su, amma ana zargin suna haifar ɗabi’un da ba su dace ba.

El-Mustapha, ya buƙaci shugabannin al’umma da jami’an tsaro su taimaka wajen tabbatar da wannan doka.

“Muna roƙon sarakunan gargajiya, ‘yan sanda, Hisbah da masu tsaron unguwanni su haɗa kai da mu wajen tabbatar da bin wannan umarni,” in ji shi.