Gwamnatin Jihar Kano ta haramta shan Shisha da kuma kasuwancinta a fadin jihar.
Manajan Daraktan Hukumar Yawon Bude Ido ta Jihar, Yusuf Ibrahim Lajawa, ya ce an yi hakan ne a kokarin gwamnatin jihar na yakar miyagun dabi’u masu alaka da aikata miyagun laifuka a jihar.
- Dalilin da nake so a soke lefe da kayan daki — Fauziyya D. Sulaiman
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace 50 a kauyen Kaduna
“Mun fara daukar mataki a kan masu kasuwancin wadannan abubuwan domin tabbatar da ba saba dokar da za ta fara aiki nan ba da jimawa ba,” inji shi.
Ya sanar da haka ranar Juma’a, yana mai bayyana cewa a shirye gwamnatin take ta kakkabe ayyukan assha da ke kai matasan jihar ga aikata laifuka.
Tun a ranar 3 ga watan Nuwamba, 2021 ne Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya rattaba hannu kan dokar haramta bayar da dakunan otel ga yara ’yan kasa da shekara 18 a jihar.
Dokar wadda za ta far aiki a shekarar 2022 ta shafi masu wuraren da ake gudanar da tarukan biki sannan ta haramta kasuwancin shisha da giya.