Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da ɗage ranar komawa Makarantun Firamare da Sakandare kamar yadda aka tsara a ranar 8 da 9 ga watan Satumba.
A wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na Jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa ɗage komawa makarantun ya zama dole ne, saboda wasu dalilai na gaggawa da za su taimaka wajen samar da yanayin karatu mai inganci ga ɗalibai.
- Tsadar Rayuwa: Dole ce ta sa muka ɗauki matakai masu tsauri — Tinubu
- Yadda shugabanni ke taimakon ’yan bindiga suna kashe mutane a Katsina — Radda
Ya tabbatar da cewa za a sanar da sabuwar ranar komawa makarantu nan ba da jimawa ba.
“Mun fahimci cikas ɗin da wannan mataki zai iya haifarwa ga iyaye da ɗalibai, amma dole ne a ɗauki wannan mataki domin inganta yanayin karatun yara,” in ji Doguwa.
Ma’aikatar ta yi kira ga iyaye, ɗalibai, da su yi haƙuri tare da fahimtar yayin da gwamnatin ke ƙoƙarin kammala gyare-gyare a makarantun faɗin jihar.
Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, ya fara gyara ajujuwa da sauran gine-gine a faɗin makarantun Kano.
Kazalika, gwamnatin ta bayar da kwangilar ɗinka wa ɗalibai kayan makaranta da sauran abubuwan amfanin ɗaukar karatu.