✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Gwamnatin ta ce za ta gurfanar da waɗanda ba sa biyan haraji a gaban kotu.

Gwamnatin Jihar Kano, ta ce tana fatan samun sama da Naira biliyan 20 a kowane wata uku na shekarar 2025, wanda zai kai jimillar sama da Naira biliyan 80 a shekarar.

Haka kuma, gwamnatin ta sanar da shirin gurfanar da waɗanda suka ki biyan haraji a gaban kotu, a wani yunkuri na inganta tsarin karɓar haraji a jihar.

Shugaban Hukumar Karɓar Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dokts Zaid Abubakar ne, ya bayyana hakan yayin gabatar da bayani a wani taron bita na manyan jami’an gwamnatin jihar.

Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya tabbatar da hakan.

Dokts Abubakar, ya ce waɗannan sauye-sauyen ba wai don ƙara yawa. haraji ba ne, na da kuma nufin inganta yadda ake tattara haraji da kuma tabbatar da cewa kowa yana biyan haƙƙinsa.

Ya kuma bayyana cewa, hukumar ta samu gagarumar nasara a ƙarshen 2024 bayan gwamna ya sauke tsohon shugaban hukumar tare da naɗa sabbin shugabanni.

Don samun ƙarin kuɗaɗen shiga a 2025, gwamnan na shirin ƙaddamar da sabon tsarin karɓar haraji a jihar.

Wannan tsarin yana da nufin samar da ƙarin kuɗaɗen shiga, wanda zai bai wa gwamnatin damar cika alƙawuranta a ɓangaren ilimi, lafiya, da inganta ababen more rayuwa.