Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a yankin Nasarawa da Trikania da ke Karamar Hukumar Chikun ta jihar.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Samuel Aruwan ya fitar, inda ya ce a yanzu dokar za ta fara aiki ne daga misalin karfe 7:00 na dare zuwa karfe 7:00 na safe, daga ranar Laraba.
Aruwan ya ce matakin ya biyo bayan sanya ido da kuma tantance al’amura daga hukumomin tsaro suka yi a yankunan.
“Daga ranar Laraba, 5 ga Afrilu, 2023, dokar za ta fara aiki daga karfe 7:00 na dare zuwa 7:00 na safe.”
Ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su ci gaba da gudanar da harkokinsu a tsakanin wannan lokaci.
Sannan ya shawarce su da su bi dokar hana fita da kuma gudanar da aiki cikin tsari yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankunan don tabbatar da tsaro da kare dukiyoyi.