Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci dukkan makarantun sakandiren gwamnati da na masu zaman kansu a jihar da su sake budewa daga ranar Litinin, daya ga watan Fabrairun 2021.
Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Misis Phoebe Yayi ce ta sanar da umarnin a wata sanarwa da ta fitar, sai dai ta ce daliban azuzuwan JSS 1 da JSS 3 da kuma SS 3 ne kawai za su dawo makaranta.
Kazalika, Misis Phoebe ta ce gwamnatin za ta sanar da ranar komawar daliban aji hudu, biyar da kuma shida na makarantun firamare nan ba da jimawa ba cikin kiyaye sharuddan kariyar COVID-19.
Ta ce gwamnatin ta dauki matsayar ne bayan zuzzurfar tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan cutar, la’akari da sake barkewarta a karo na biyu.
Sanarwar ta ce, “A sakamakon haka, Ma’aikatar Ilimi ta umarci dukkan Shugabannin Makarantun na Sakandire su yi dukkan shirye-shiryen da suka kamata wajen karbar daliban ranar Litinin.
“Sai dai Kwamitin Kar-ta-kwana na Yaki da Cutar a Jihar zai ci gaba da zagayawa domin tabbatar da makarantun lafiya kalau suke, sannan kuma suna bin dukkan matakan kariyar da gwamnati ta gindaya musu.
“Kazalika, dukkan masu makarantun sakandire masu zaman kansu dole ne suma su kiyaye wadannan ka’idojin.
“Duk makarantar gwamnati ko mai zaman kanta da muka samu ta karya wadannan dokokin za mu rufe ta nan take, ba tare ma da mun sanar da ita ba,” inji sanarwar.