Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin Naira 72,000 ga ma’aikatan jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Malam Ibraheem Musa ya fitar a ranar Lahadi.
- Na gode wa Gowon kan yadda ya ceto rayuwata a hannun Abacha — Obasanjo
- Wanda ya auri ’yar tsana shekaru 6 har yanzu yana son matarsa
Ya ce: “Ƙaramin ma’aikaci a Jihar Kaduna ya karɓi Naira 72,000 a matsayin sabon albashi na watan Nuwamba. Wannan ya nuna cewa an cika dokar sabon mafi ƙarancin albashi.”
Ya bayyana cewa abin da NLC ke nema na “ƙarin albashi” ya sha bamban da sabon mafi ƙarancin albashi,” in ji shi.
Ya ce, “Jihar Kaduna tana biyan sabon albashi, amma ƙarin albashi ba wajibi ba ne.”
Malam Musa, ya kuma yi bayani kan yanayin kuɗaɗen shiga na jihar.
Ya ce, “Jihar Kaduna tana samun jimillar Naira biliyan 12 a kowane wata, amma Naira biliyan 6.3 na tafiya a biyan albashi, sai kuma Naira biliyan huɗu da ake biyan basussuka da ita.
“Naira biliyan biyu ce kacal ke raguwa, wadda ake yin ayyukan bunƙasa jiha da ita.”
Ya ce ba daidai ba ne a kashe sama da kashi 90 na kuɗaɗen da ake samu a wasu abubuwa ba.
“Akwai mutane sama da miliyan 10 a Jihar Kaduna da suke da haƙƙin cin moriyar kuɗaɗen gwamnati,” in ji shi.
Gwamnatin ta bukaci NLC su yi haƙuri kan batun ƙarin albashi.
“Gwamna Uba Sani yana da alaƙa mai kyau da ma’aikata, kuma ya samar da motoci kyauta don jigilar ma’aikata a matsayin tallafi ga matsalolin da suka shafi tattalin arziƙi,” a cewarsa.