Gwamnatin Jihar Kaduna ta amince a bude manyan makarantun dsa ke jihar daga ranar Litinni 25 ga Janairun 2021.
Ma’aikatar Ilimin Jihar ta sanar da hakan ne bayan kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar ya kammala bincikensa a kan manyan makarantun don tabbatar da sun tanadi duk matakan dakile yaduwar cutar.
Sanarwa da Sakatariyar Ilimin Jihar, Phoebe Sukai Yayi ce ta fitar ranar Lahadi ta bayyana cewa dole manyan makarantun su bi dokoki da ka’idojin da gwamnati ta shimfida musu.
Dole ne kuma manyan makarantun su tanadar da na’urar gwada dumin jiki, sinadarin wanke hannu, bayar da tazara, sannan dalibai da ma’aikata su kasance a koda yaushe sanye da takunkumi.
Ta kara da cewa dole ne a gujewa samun cunkoso a azuzuwa da kuma dakunan kwanan dalibai.
Kazalika, kwamitin yaki da cutar zai rika kewaye lokaci zuwa lokaci a makarantun don sanya ido kan kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka sanya.
Phoebe ta yi fatan alheri da jinjina game da irin hadin kai da makarantun ke ba wa Gwamnatin Kaduna inda ta sanar cewa kwamitin yaki da COVID-19, na nazari kan yadda za a sake bude kananan makarantun gwamnati da na kudi a fadin jihar.