Majalisar Zararwar Jihar Jigawa da sahale a gina ajujuwa a makarantun Islamiyya a kan Naira miliyan 500.
Majalisar ta amince ne bayan Ma’aikatar Ilimin Matakin Farko ta gabatar da bukatar ba da kwangilar gina ajujuwa 132 makarantun Islamiyya da ke mazabu 30 a jihar.
Za a gina ajujuwan Islamiyyan guda 132 ne a karkashin shirin ayyukan mazabe na na shekarar 2024 da muke ciki.
Gwamnatin jihar ta kuma amince tare ba ba da umarnin aiwatar da shawarwarin kwamatin da ta kafa kan Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Bilyaminu Usman da ke Hadejia, nan take.
- Matsalar tsaro: Sarkin Kano ya kalubanci minista kan amfani da fasaha
- Ra’ayin Kanawa kan sulhun Ganduje da Kwankwaso
Hakazalika ta sahale kafa kwamitin riko a makarantun gaba da sakandare hudu da ke jihar — Kwalejin Ilimi da ke Gumel, Kwalejin Ilimi, Shari’a da Ilimin Musulunci da ke Ringim, Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Jigawa da ke Dutse da kuma Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Bilyaminu Usman da ke Hadejia.