✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ra’ayin Kanawa kan sulhun Ganduje da Kwankwaso

Masu rike da mukaman jam’iyyar na jihar za su gana a ranar Alhamis kan lamarin sulhu

Mazauna Kano sun bayyana yunkurin sasanta jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin abin maraba.

Sakataren APC a Jihar Kano, Zakaria Sarina, ya tabbatar da cewa masu rike da mukaman jam’iyyar na jihar za su gana a yau Alhamis kan abin da ya danganci sulhun.

Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu, a ganawarsa da Ganduje da Kwankwaso a lokuta daban-daban, ya bukaci kowannensu ya gana da manyan masu ruwa da tsakin bangarensa game da lamarin sulhun da ake sa ran zai jagoranta a nan gaba.

Batun sulhun dai ya samu amincewa Kanawa irin su Abubakar Ilyasu Yakasai, wanda ya ce, Talakawa na kallon wannan ci gaban da sha’awa. Addu’armu ita ce Allah ba mu shugabanni nagari wadanda za su yi mana aiki domin cigabanmu, su maganci mana matsalolinmu.”

A cewarsa, duk da cewa an maraka, amma sulhun shi ne mafi alheri, domin ya kamata a ce sun dade da rungumar juna.

Shi kuwa Isa Abubakar, hadewar NNPP APC da APC a Kano zai zama abin farin ciki, saboda “adawar siyasa da yakin baka tsakanin NNPP da APC za su tsaya a kare muradun jama’ar Kano baki daya. Ina goyon bayan sulhu”.

Wani mazaunin garin, Saifullahi Awwalu, na ganin cewa sulhun zai kawo karshen rikicin siyasa a jihar tsakanin ’yan uwa.

Wannan ra’ayin nasa yana daidai da na wata mace wacce ta bayyana kanta a matsayin Nana.

Sai dai Sunusi Isa ya ce sulhun takobi ne mai kaifi biyu, wanda a cewarsa, zai iya zama maslaha ga Kano ko kuma kawai tausasa kishin Ganduje da Kwankwaso.

Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC Hausa cewa, Tinubu ya umarci shugabannin jam’iyyar da su saurari duk wanda ke son shigowa jam’iyyar, ba Rabiu Kwankwaso kadai ba,

Abdullahi Abbas yana mai cewa idan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na son shiga jam’iyyar, suna maraba da shi.

Amma wani na hannun daman Kwankwaso kuma jigo a NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya ce abu ne mai matukar wahala su raba mukamai da APC bayan sun yi aiki tukuru don ganin sun lashe zabe a Kano.