✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jigawa za ta dasa itatuwan zogale a asibitoci 68

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware asibitoci 68 a kananan hukumomin jihar 27 domin daddasa itatuwan zogale saboda amfanin marasa lafiya a kokarinta na samar da…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware asibitoci 68 a kananan hukumomin jihar 27 domin daddasa itatuwan zogale saboda amfanin marasa lafiya a kokarinta na samar da itatuwa masu taimaka wa marasa lafiya wajen inganta lafiya.

Sannan gwamnatin jihar ta bayar da umarnin a dasa itatuwan dalbejiya da turare a daukacin makarantun jihar a kokarinta na magance kwarorowar hamada da barnar da iska ke yi wajen yaye rufin makarantun a lokacin damina.

Babban Darakta a Hukumar Gandun Daji ta Jihar Jigawa, Alhaji Umar Idris Giginya Babura ne ya tabbatar da haka, inda ya ce gwamnatin jihar ta raini itatuwan dalbejiya da kanya da kadanya da dorawa da badala da bini-da-zugu da dakwara da bagaruwa har miliyan biyu da rabi a cibiyoyin rainon irin itatutuwa 23 da ke jihar.

Daraktan ya ce da zarar an kammala rainonsu za a raba su ga wadanda suka dace ciki har da makarantu da asibitocin jihar a kokarin gwamnatin na yaki da kwararowar hamada.

 yakarada cewar sauran bishiyoyin za adasasune abakin titunan dagwamnatin jahar ta samar dake daukacin fadin jahar domin magance barazanar Hamada da zaizayar kasa Alhaji Umar Giginya Babura, ya kara da cewar gwamnatin jihar za ta farfado da cibiyoyin rainon irin itatuwa da suka jima ba sa aiki, domin ci gaba da aikin rainon irin. Cibiyoyin  su ne na garin Bulangu da Majeri da Guri da Kumsa, yayin da gwamnatin za ta gina wasu sababbin cibiyoyin rainon iri a garin Miga da Gwiwa.

Daraktan ya ce jihar ta yi doka cewa daga yanzu duk wani aikin gwamnatin jihar da za a kaddamar ya zama wajibi, sai an dasa itatuwa a wurin kafin Gwamna ko wani jami’in gwamnati ya kaddamar.

Da ya koma Koriyar Katanga da ta zagaya Afirka wadda a Najeriya ta fara daga Jihar Kebbi zuwa Jihar Borno yanzu a Jigawa dashen itatuwan Koriyar Katangar ya kai kilomita 64 a kananan hukumomi shida na jihar da suka hada da Babura da Sule Tankarkar da Maigatari da Birniwa da Gumel. Kuma ya ce Gwamnatin Tarayya ta samar da famfuna masu aiki da hasken rana a kauyuka 21 da suke wadannan kananan hukumomi shida.

Daraktan ya ce an gudanar da dashen itatuwan ne tare da samar da famfunan ne domin a bai wa mutanen da suke kan iyaka ruwan sha tare da bai wa itautuwan da aka dasa ruwa.

Ya ce a bana za a ci gaba da aikin dashen itatuwan na Koriyar Katanga ce a iyakokin kananan hukumomi uku da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar da suka hada da Kaugama da Maigatari da kuma Birniwa.