A shirin tallafawa mata da gwamnatin Jigawa ta fara shekara hudu da suka gaba ta, Gwamnatin jihar ta bayar da bashin akuyoyi dubu 25,605 ga matan jihar dubu 8,535.
An dai fara shirin bayar da bashin akuyoyi ga mata ne lokacin hawan wannan gwamnati, a shirin ana baiwa mata bunsuru daya da akuya biyu yayin da zasu biya bayan watanni 18 a matsayin tallafi.
Wanda ta jagoranci kaddamar da rabon akuyoyin uwargidan Gwaman jihar Jigawa Hajiya Magajiya Muhammad Badaru Abubakar a garin Kafin Hausa ta karawa matan jihar da tallafin kudi na Naira dubu 5.
Magajiya ta ce, a farkon shirin an baiwa mata dubu 5,740 daga kananan hukumomi 16 na jihar inda suka samu akuyoyi dubu 17, 220.