✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jigawa ta ja kunnen ’yan Hisba

Gwamnatin Jihar Jigawa ta hori jami’an Hisba na kananan hukumomin jihar kan su guji yin sakaci da aikinsu Jawabin hakan ya fito ne daga bakin…

Gwamnatin Jihar Jigawa ta hori jami’an Hisba na kananan hukumomin jihar kan su guji yin sakaci da aikinsu

Jawabin hakan ya fito ne daga bakin Mai bai wa Gwamnan Jihar Shawara a kan Harkokin Addini Alhaji Mustapha Sale kwalam a wajen wani taro da ya yi da jami’an Hisbar a ranar Litinin da ta gabata.

Ya ce duk dan Hisbar da aka samu da yin sakaci da aikinsa gwamnatin jihar za ta yi waje da shi

Mashawarcin Gwamnan ya ce idan har za su yi aikinsu kamar yadda doka ta tanada babu shakka sauran ma’aikatan tsaro za su samu saukin gudanar da ayyukansu. Kuma ya hori dogarawan Hisba da su tona duk wani batagari da yake wasa da aikinsa da duk jami’an da ba sa zuwa aiki domin a yi waje da su.

Kwamamdan Hisba na Jihar Jigawa Alhaji Ibrahim dahiru Garki ya nemi gwamnatin jihar ta agaza wa hukumar da motocin sintiri da kuma babura domin gudanar da aikinsu cikin sauki.

Alhaji Ibrahim dahiru ya ce suna fama da karancin motoci da babura a hukumar wanda hakan ke kawo musu cikas wajen aiwatar da ayyukansu.

Ya yaba wa gwamnatin jihar kan hana ’yan siyasa tsunduma baki ko yi wa hukumar ta Hisba katsalanda a cikin harkokinta. Kuma ya gode wa shugabannin kananan hukumomin jihar 27 saboda irin gudunmawar da suke bai wa hukumar.