A wani yunkuri na kawo sauyi ga ilmin almajirai, Gwamnatin Gombe za ta fara daukar bayanan makarantun Tsangayan jihar da tantance almajiransu da nufin tantance adadinsu da kuma jihohin da suka fito.
Gwamnatin Gombe za ta fara tantance makarantun Tsangaya da ba wa almajiran jihar katin shaida a kokarinta na inganta karatun allo
Sayyada Aminatu Sheikh Dahiru Usman Bauchi, mai bai wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya shawara kan harkokin Tsangaya da Almajirai, ita ce ta bayyana haka a tattaunawarta da wakilinmu.
Ta bayyana cewa ofishinta zai nemi izinin gwamnati tare da hada kai da Hukumar Kula da Shaida ta Kasa (NIMC) domin yi wa daukacin almajirai rajista a jihar.
- Abba ya raba wa masu talla a titun Kano tallafin N50,000
- Kotu ta kwace gidajen N11bn a hannun Emefiele
- Uba ya sayar da ’ya’yansa biyar a Sakkwato
Sayyada Aminatu ta kara da cewa idan aka kammala za a ba wa almajiran katin shaida domin saukaka zirga-zirgarsu ba tare da tsangwama ba.
Ta ce, “Idan muka yi musu rajista, za a ba su katin shaida kuma za su kasance ba tare da wata barazana ba.”
Sayyada Aminatu bayyana takaici bisa dabi’ar wasu iyaye da suka yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar tura ’ya’yansu makarantun Tsangaya ba tare da wani tanadi ko tsari da ya dace ba.
Hakan a cewarta ya sa yaran sukan wayi gari ba zu da wani zabi face su zama su ne masu kula da kansu da daukar nauyn kansu.
Ta ci gaba da cewa, “Kowa ya san tsarin ilimi ya canza, amma ana ganin wadannan yara kanana suna yawo a kan tituna, sun zama matsala a tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama’a saboda rashin ilimin boko.
“Abin takaici ne ganin yadda almajirai ke kwana a wuraren tashohin motoci da kasuwanni; ba su ba su da hanyar rayuwa saboda tsadar rayuwa.”