✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya raba wa masu talla a titun Kano tallafin N50,000

Gwamnan Kano Abba Yusuf ya raba wa mata da mata 465 da ke sana'ar talla a kan tituna tallafin Naira dubu hamsin-hamsin.

Gwamna Abba Yusuf ya raba wa mata da matasa 465 da ke tallar kaya a kan titunan Kano tallafin Naira dubu hamsin-hamsin.

Gwamnan ya bayyana cewa manufar rabon tallafin da aka yi ranar Laraba shi ne kara wa masu kananan sana’o’in karfin jari domin dogaro da kansu.

Wadanda suka amfana sun hada da masu sayar da kayan mota da kayan girki da sauransu da ke yawo da kayan a kan tituna inda gwamnan ya yaba musu bisa dagewarsu wajen neman na kansu.

Abba ya bayyana cewa rukuni tara na masu karamanin ne za su amfana da irin tallafin, wanda “kari ne a kan Naira dubu hamsin-hamsin da aka raba wa mata da mata 5,200 domin dogaro da kansu.

“Shirin ya haifar da kyakkyawan sakamko inda ya kara wa wadanda suka amfana karfin jari.”

Daga nan ya bukaci wadanda suka amfanan da su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta dace domin bunkasa sana’o’insu.