✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Filato za ta hukunta mutanen da suka fasa rumbunan ajiye abinci

Sakataren ya ce jami’an tsaro suna nan suna farautar wadanda suka fasa wuraren ajiye abincin.

Gwamnatin jihar Filato ta kafa kotuna guda 7, don hukunta mutum 307,  da ake tuhuma da fasa rumbunan da aka ajiye abincin tallafin COVID-19, a wurare daban-daban a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Atu ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, a gidan gwamnatin jihar da ke Jos, a ranar Litinin.

Gwamnati ta yanke hakan ne bayan kammala taron gaggawa da Majalisar Tsaron jihar ta kira, kan yadda aka yi kwanaki biyu, ana fasa rumbunan da aka ajiye abincin tallafin COVID-19, tare da sace abincin da bata wasu kadarorin gwamnatin jihar.

Sakataren ya ce jami’an tsaro suna nan suna farautar wadanda suka fasa wuraren ajiye abincin tare da sace abincin, don ganin an kamo su an hukunta su tare da dawo da kayayyakin abincin da aka sace.

Ya ce ya zuwa yanzu hankula sun fara kwantawa a jihar, amma duk da haka akwai barazanar bata garin za su iya kaiwa wasu kadarorin gwamnati da wuraren kasuwanci na masu zaman kansu hari.

Don haka an umarci jami’an tsaro su kara tsaurara bincike a dukkan shingayen jami’an tsaro a kananan hukumomin Jos ta Arewa, da Jos ta Kudu, don ganin ana aiki da dokar hana fita da aka kafa.

Sakataren gwamnatin ya gargadi al’ummar jihar su guji amfani da wadannan kayan abinci, da aka sace, saboda suna dauke da gubar maganin da zata iya cutar da duk wanda ya yi amfani da kayan abincin.