Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Filato kuma dan majalisa mai wakiltar Mazabar Dengi, Malam Saleh Shehu Yipmong, ya ce Gwamnatin Jihar tana kokarin ganin kowa ya kama sana’a a jihar, don mutane su samu abin da za su dogara da kansu.
Mataimakin Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen bude wurin sana’ar daukar wakoki da fitaccen mawakin ’yan siyasar nan da ke Jos, Murtala Abdullahi Mamsa, ya yi a garin Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa.
Mataimakin Shugaban ya ce don haka Majalisar Dokokin Jihar, ta yi doka kuma Gwamnan Jihar, Mista Simon Lalong ya sanya hannu kan kafa Hukumar Tallafa wa Masu Kananan Masana’antu a Jihar.
Ya yi kira ga wadanda suke da sana’o’i a jihar su yi kokari su kafa kungiyoyi, domin su amfana da wannan tallafi da Gwamnatin Jihar ta fito da shi.
Malam Saleh Yipmong ya ce ya kamata duk abin da mutum ya kama a matsayin sana’a, ya rike shi da mutunci. Domin ta haka ne sana’ar za ta bunkasa.
“Babu shakka wannan wurin sana’ar daukar wakoki da aka bude, zai taimaka wa matasa da dama, su samu aikin yi. Idan ana samun irin wadannan wurare na samar da ayyukan yi, zaman banza zai ragu a kasar nan, don haka muna yaba wa wanda ya bude wannan wuri,” inji shi.
Tun farko a jawabin Malam Murtala Abdullahi Mamsa, ya ce rufin asirin da ya samu ta sanadin waka ne, ya karfafa masa gwiwar bude wurin don bunkasa wannan sana’a.
Ya ce a wannan wuri, suna sa ran za su yi gogayya da Kano, wajen daukar wakoki domin suna da kayayyakin aiki na zamani masu inganci, da za su rika yin amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
Har ila ya ce a wannan wuri, sun bude tashar talabijin ta Online, wadda za su rika gayyato manyan malamai da manyan ’yan siyasa suna tattaunawa da su, kan abubuwan da za su amfani jama’a.
Taron ya samu halartar manyan ’yan siyasa da sarakuna da ’yan kasuwa daga wurare daban-daban, na Jihar Filato.