Gwamnatin Jihar Filato ta kara wa ma’aikatan jihar 5,858 girma a wuraren ayyukansu. Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na Jihar, Malam Muhammad Nazifi Ahmad ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron ’yan jarida na wata-wata da ma’aikatarsa ke shirya wa kwamishinonin ma’aikatun jihar. Ya ce su ma malaman makarantun jihar, gwamnatin ta Filato ta kara wa 1,067 girma. Haka kuma gwamnatin ta sanya sunayen tsofaffin ma’aikatan jihar 515 a tsarin biyan fensho. Ya ce gwamnatin ta yi wadannan abubuwa ne, don ganin ta kyautata wa ma’aikatan tare da tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Hakazalika ya ce gwamnatin jihar ta tashi tsaye wajen magance matsalar ruwan sha a jihar musamman a garin Jos da kewaye. Ya ce ya zuwa yanzu an fara samun ruwan sha a wuraren da suka yi sama da shekara 20 babu ruwa sha a garin Jos. Kuma an bayar da aikin haka rijiyoyin burtsatse guda 340 a kananan hukumomin Riyom da Shendam tare da biyan kudin magungunan da za a rika sanya wa a ruwan da ake bai wa al’ummar jihar har na tsawon shekara 4.
Haka kuma ya ce a kokarin gwamnatin jihar na ganin ta bunkasa harkokin noma a jihar, a daminar bana, ta sayo takin zamani tirela 777 ta raba wa manoman jihar kan farashi mai rahusa. Haka kuma ganin jihar ita ce kan gaba wajen noman dankalin Turawa, ta kawo sabon irin dankalin ta raba wa manoma, Kuma ta fito da tsarin adana dankalin Turawan da tumatir da sauran kayayyakin amfanin gona na marmari don kada su lalace.
Gwamnatin Filato ta kara wa ma’aikata dubu 5 da 858 girma
Gwamnatin Jihar Filato ta kara wa ma’aikatan jihar 5,858 girma a wuraren ayyukansu. Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na Jihar, Malam Muhammad Nazifi Ahmad ne…