Ko hayaniyar da ake ta yi da murnar Buhari ya ziyarci Jihar Kano ai shirme ne. Domin da yaya ya amince ya kai ziyarar? Ba sai da aka takura masa, aka tursasa masa, surutu da maganganun Kanawa da korafe-korafensu sun game ko’ina, cewa su ne jihar da suka fi ba shi kuri’a a zaben shekarar 2015, amma ya manta da su, kuma gwamnatinsa ba ta yi musu komai ba, sannan aka ba shi shawara cewa ya kamata ya je Kano, sannan ya kai ziyarar?
Imamu Ahmad da Imam Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA), ya ce; “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce da Ka’ab bin Ujrata (RA): “Allah Ya tsare ka, Ya kiyaye ka, ya kai Ka’ab daga riskar shugabancin ashararai, wawaye; sai Ka’ab ya ce: “Mene ne shubagancin ashararai, wawaye, ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce: “Wadansu shugabanni ne da za su zo nan gaba, ba sa bin shiriyata, kuma ba sa bin tafarkina. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyarsu da yaudararsu, kuma ya taimake su a kan zaluncinsu, to, ba ya tare da ni, kuma ni ma ba na tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyarsu da yaudararsu ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to wadannan suna tare da ni, kuma ni ma ina tare da su, sannan za su sha ruwan tafkina…..” (Ahmad da Al-Bazzar ne suka ruwaito).
A wani Hadisin, Annabi (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsayu ba har sai ya kasance munafukan cikin al’umma da wawayenta su ne suke yin shugabanci.” (dabarani ne ya ruwaito)
Munafukai da wawaye za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, barayi ko masu ba barayi kariya saboda ’yan jam’iyyarsu ne ko saboda wata maslaha tasu ko ta wasunsu.
Annabi (SAW) ya fadi a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa: “Lallai yana daga alamomin kusantowar Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.” (Imam Hakim ne ya ruwaito a Al-Mustadrak)
Ya ku ’yan Najeriya! A yau duk wanda yake raye shaida ne shi a kan cewa lallai duk abin da Annabi (SAW) ya ba da labari shi ne yake faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantarmu, face ’yan kadan daga cikinsu, ashararai ne.
Saboda haka ya zama wajibi kowa ya yi kokari ya ba da gudunmawa gwargwadon ikonsa, don ya zamo wadanda za su shugabance mu a nan gaba su zamo mutanen kirki ne. Sannan maganar a yi SAK ta kare, kowa halinsa da abin da ya tabuka wa jama’a ne zai fisshe shi. Maganar a labe a bayan Buhari a cuci al’umma ta kare da ikon Allah. Dukanmu dai shaidu ne, mun ga illar yin SAK da sharrinsa da rashin alfanunsa. Ko wannan wahalar da wannan aya da wadannan gwamnoni suke gasa wa mutane a hannu sun isa su sa mu gane illar SAK da kuma sharrinta. Dubi yadda gwamnonin nan suke yin abin da suka ga dama, Buhari ya ki daukar kwakkwaran matakin da ya dace a kansu, sai dai ya lallashe su. Shin muna ganin gwamnonin nan za su iya yi wa mutum irin Obasanjo haka, ba tare da ya dauki mataki a kansu ba? Amma dubi yadda suka raina Buhari, don sun san cewa ba ya iya yin komai! DON HAKA WALLAHI BABU WATA MAGANAR SAK, CANCANTA KAWAI!
’Yan uwana ’yan Najeriya! Mu sani lokacin yin shiru ya wuce, ba zai yiwu ba a ce galibin mutanen banza ne ke jagorantarmu. Mu sani, dukanmu Allah zai kama mu da laifin rashin tabuka komai kan samar wa al’umma nagartattun shugabannin siyasa. A yau dukanmu shaidu ne a kan irin halin da kasarmu da yankinmu mai albarka na Arewa suka shiga, saboda rashin shugabanci nagari. Shugaban kasa dan Arewa ne, to amma don Allah wane yanki ne ya fi talauci da rashin aikin yi da matsaloli a kasar nan idan ba Arewar? To abin da ya faru dai ya riga ya faru, yanzu abin tambaya shi ne; me muke yi domin kokarin samar da shugabanni na kwarai masu amana, masu tausayi da kishin talakawansu a nan gaba? Ko har yanzu barci muke yi ba mu farka ba?
Ya ku bayin Allah! Mu sani lallai asalin shugabanci shi ne; a shugabantar da wanda ake ganin ya dara kowa ilimi da adalci da gaskiya da amana da rashin nuna bambanci, mai kokarin hada jama’a da rashin son kai, mai kishin kasa kuma gogagge, jarumi, mai iya daukar mataki cikin lokaci, mai sakin hannu, mai kyauta, mai alheri, mai kokarin samar da arziki ga ’yan kasa da sauransu. To amma a yau abin ba haka yake ba, domin mafi yawanci, fasikai, mutanen banza, ashararai, mayaudara, mashaya, barayi, wadanda ba su san kimar dan Adam ba, masu kuntatawa da tsananta wa talaka, masu rike hannu, su ne ke shugabantarmu. Saboda suna da kudi, ko don dangartakarsu, ko wani matsayi da suke da shi, ko saboda tsabagen rashin kunyarsu, ko don ’ya’yan manya ne su, amma ba don cancanta ba. Duk wannan saboda lalacewar al’amura ko saboda mutanen kirki na gaskiya sun mika musu wuya, sun kame hannuwa, sun zama matsorata, sun ce babu ruwansu da siyasa, sun yarda mutanen banza sun ci su da yaki.
Ya ku bayin Allah! Kamar yadda ya gabata, hudubarmu tana tsokaci ne a kan cewa; “Ba za ka taba samun mutanen kirki masu gaskiya suna zabe ko goyon bayan zulunci da azzaluman shugabanni ba.”
Allah (SWT) Ya yi umarni da adalci da goyon bayan adalai a duk inda suke, kuma Ya yi hani da zalunci da goya wa zalunci da azzalumai baya a duk inda suke. Allah Ya fada a cikin LittafinSa Mai girma cewa: “Lallai Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa da bai wa ma’abucin zumunta (hakkinsa), kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci. Yana yi muku gargadi, tsammaninku kuna tunawa.” (Nahli: 90)
Kuma Allah Yana cewa: “Kada ku karkata zuwa ga (ku goyi baya/ko ku zabi) wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wadansu majibinta baicin Allah, sannan ba za a taimake ku ba.” (Hud:113)
Ya ku Musulmi! Lallai cikin wadannan ayoyi masu girma, mun ga yadda Allah Ya umarce mu da tsaida adalci da kuma cewa kada mu yarda mu goyi bayan azzalumai. Mahaliccinmu Ya tabbatar da cewa in muka ki bin umurninSa, to, lallai azabar wuta za ta shafe mu tare da azzaluman da muka goyi bayansu.
Allah Ya albarkaci wannan kasa da duk nau’o’in albarkatu, amma saboda zalunci da cin hanci da rashawa da rashin adalcin shugabanni, an wayi gari kasar tana neman rushewa. A yau kowane fanni ka duba za ka ga ba inda zalunci da cin hanci da rashawa ba su yi katutu ba. Kuma babban bala’in ma shi ne goyon bayan masu zaluncin don abin duniya, ko wata bukata ta kashin kai. Wannan ya jawo ba a gudun aikata zalunci, domin mutane sun san duk zaluncin da za su yi, duk satar da za su yi, matukar suna da abin hannu, ko suna da daurin gindi, to al’umma za ta karbe su hannu bibiyu, a girmama su, a ba su sarautun gargajiya ko digirin girmamawa ko wani matsayi a cikin al’umma. Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!
Ku sani lallai idan aka wayi gari al’umma ta zama haka, to sai dai a ce Allah Ya kiyaye, domin kashinta ya bushe, sai buzun ta. Tabbas Allah zai jarrabi wannan al’umma da abubuwa marasa dadi iri-iri, kamar yadda muke gani, muke ji, kuma muke dandanawa a yau.
Imam Ibnu Kasir a yayin da yake bayani game da ayar da ta yi hani a kan goyon bayan azzalumai da ke cikin Suratul Hud: 113, ya ce: “Fadin Allah cewa, “Kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku.” Aliyu bin dalha ya ruwaito daga dan Abbas (RA) cewa, ma’anarta: “Kada ku mika wuya ga azzalumai.”
Imam Al-Aufiy kuwa ya ruwaito daga dan Abbas (RA), cewa: ma’anarta: “Kada ku karkata da goyon bayan shirka da zalunci.”
Kuma Abul-Aliyah ya ce, ma’anarta, “Kada ku yarda da aikin zalunci da ayyukan azzalumai.”
Shi kuwa Imam Ibnu Jarir ya ruwaito daga dan Abbas (RA) cewa, ma’anarta: “Kada ku karkata ku goyi bayan azzalumai.”
A karshe Ibnu Kasir ya ce, zance mafi kyau game da fassarar ayar, shi ne; “Kada ku taimaki azzalumai a kan zaluncinsu, ta hanyar goyon bayansu. Domin duk wanda ya aikata haka, to ya yarda da aikinsu na zalunci ke nan.”
Kuma an ruwaito cewa: “Wani babban malami daga cikin magabata da ake kira Al-Muwaffik, wata rana yana Sallah a bayan wani limami, sai limamin ya karanta Suratul Hud, da ya kawo daidai aya ta 113 inda Allah ke cewa: “Kada ku karkata ga wadanda suka yi zalunci (azzalumai), wuta za ta shafe ku.” Sai Al-Muwaffik ya fadi kasa ya suma, lokacin da ya farfado sai aka tambaye shi, me ya faru? Sai ya ce, “Wannan ayar tana nufin Allah zai azabtar da wanda ya goyi bayan azzalumi ne, to ina ga shi azzalumin kansa?” Sai ya ce wannan ne na tuna da shi ya tsoratar da ni, hankalina ya tashi ya sa na suma.”
Saboda haka ya ku ’yan Najeriya! Mu ji tsoron Allah, mu sani ba za mu kawo karshen zalunci ba, har sai mun daina goyon bayan mulkin azzalumai da mulkin danniya. Sai mun kyamace su da abin da suka mallaka. Amma muddin azzalumi zai yi zalunci ya tara abin duniya ta hanyar zalunci, kuma mu je muna kwadayin wannan abin nasa, muna girmama shi saboda abin duniya, to ba yadda za a yi zalunci ya kare a cikin al’umma.
Allah Ya sani, mun yi wa wadannan shugabanni kyakkyawan zato, cewa da ikon Allah idan sun zo za su gyara kasar nan, su iya samar da canjin da muka jima muna nema. Mun nuna masu so da kauna, mun yi musu kamfen, mun zabe su. Sun dauki alkawura cewa za su kau da matsalolin da suke damunmu. Wasunmu sun rasa rayuka wajen zaben nan, wadansu sun rasa hannu, wadansu kafa, wadansu dukiyoyinsu. Amma bayan sun hau mulki da shekara biyu da rabi, sai muka ga sabanin haka, sai ga shi yanzu abubuwa suna faruwa marasa kyau, marasa dadi a gwamnatocinku, kuna kokarin gaya mana ai kaddarar Allah ce!
Ya Allah ’yan uwanmu mutanen jihohin Borno da Yobe da Adamawa Zamfara da sauran jihohi da garuruwan da Ka jarabce su da fitinu da tashe-tashen hankula, Ka kawo musu saukin wannan wahala. Ya Allah Ka jikansu, Ka tausaya masu Ka sa duk wannan wahala ta zama kaffara a gare su. Ya Allah Ka albarkace su da mu baki daya da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ka wadata kasarmu Ka zaunar da mu lafiya. Ya Allah Ka yi mana maganin satar mutane domin samun kudin fansa a kasar nan, amin.
Mun tsakuro ne daga hudubar Imam Murtada Muhammad Gusau, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Nagazi-Ubete, Okene, Jihar Kogi, ta ranar Juma’a 19 ga Rabi’ul Awwal, 1439 BH (8 ga Disamba, 2017)