Jam’iyyar PRP ta yi kira ga ’yan Najeriya da su dora laiin halin da Najeriya ta tsinci kanta a kan Gwamnatin Buhari.
Jam’iyyar ta ce yayin da ake kokarin shiga sabuwar shekarar 2021, kamata ya yi duk wani mai kishin kasa ya mayar da hankali wajen ceto Najeriya daga kangin kunci da take ciki.
- ‘Yunwa za ta addabi yara miliyan 10.4 a Najeriya da wasu kasashe a 2021’
- Buhari ya nemi gafarar iyayen daliban da aka sace —PDP
- Coronavirus ta kashe karin mutum 7 a Najeriya, 838 sun kamu
“Abun takaici shi ne maimakon APC ta dukufa wajen tsamo Najeriya daga halin da take ciki, sai ta bige da zargin gwamantocin baya.
“Ko da ya yaushe Buhari na alakanta gazawarsa da gwamnatocin baya,” inji shugaban jam’iyyar na Kasa, Falalu Bello.
Falalu Bello ya bayyana hakan ne a matsayin sakonsa na murnar shiga Sabuwar Shekara ga ’yan Najeriya, inda ya kara da cewar Buhari ne ya lalata Najeriya.
A cewarsa gwamnatin APC ta gaza magance matsalar tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da karuwar talauci a tsakanin ’yan Najeriya.
Ya kara da cewa dole ne ’yan Najeriya su kasance masu sadaukarwa, don ganin an gudu tare an tsira tare.
Shugaban na PRP ya ce, ya kamata ’yan Najeriya su rike tafiyar jam’iyyar domin ita ce kadai ke da nagartattun manufofi.