✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Buhari ce ta janyo hauhawar farashi a Nijeriya — Ministan Kuɗi

Gwamnatin Buhari ta yi amfani da wani tsari na ‘Ways and Means’ da ya riƙa samar mata da kuɗaɗen toshe gibin kasafin kuɗinta.

Ministan Kuɗi da Gudanar da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ɗora alhakin hauhawar farashin da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu a kan tsohuwar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Minista Edun ya ce buga takardun kuɗi na tiriliyoyin naira da Gwamnatin Buhari ta riƙa yi tsawon shekaru takwas ba tare samun wani kyakkyawan tasiri kan hakan ba shi ya haddasa matsalar da ƙasar ta tsinci kanta na matsalar tattalin arziki a yanzu.

Aminiya ta ruwaito Ministan na wannan jawabi ne a gaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dattawa a ranar Laraba.

A cewar Ministan, za su bi diddigin yadda Gwamnatin Buhari ta riƙa buga takardun kuɗi har na naira tiriliyan 22.7 da duk wata manufa da ke tattare da hakan.

Ya ce “Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta bai wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) umarnin buga takardun kuɗi har naira tiriliyan 22.7 a bisa tsarin da ake kira ‘Ways and Means’.

“Wannan tsari da Gwamnatin Buhari ta yi amfani da shi tun daga shekarar 2015 zuwa 2023 shi ya jefa Nijeriya cikin matsanancin yanayi na hauhawar farashi,” a cewar Ministan.

Ana iya tuna cewa dai Gwamnatin Buhari ta yi amfani da wani tsari da CBN ya kira ‘Ways and Means’ da ya riƙa samar mata da kuɗaɗen toshe gibin da aka samu a kasafin kuɗinta.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kuɗin na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa, ya ce za su ci gaba da gudanar da ire-iren wannan zama domin bijiro da hanyoyin da za a dakile matsalar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.