Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince wa Gwamnatin Tarayya ta sayi kashi 20 cikin 100 na hannun jarin Matatar Mai ta Dangote a kan Dala biliyan 2.76.
Minista a Ma’akaitar Mai, Timipre Sylva ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar a ranar Laraba a Abuja.
Aminiya ta gano cewa kudin hannun jarin da gwamnatin za ta saya a Matatar Man Dangoten ya kusa ninka abin da gwamatin za ta kashe a wurin gyaran matatun mana Kaduna da Warri.
Sylva ya ce Majalisar Zartarwar ta amince a kashe Dala biliyan 1.48 domin gyaran matatar mai da ke Kaduna da kuma Warri.
Gyaran matatar mai da ke Kaduna zai lakume Dala miliyan 586.9, na Warri kuma Dala miliyan 897.7, kuma an kasa yadda za a gudanar da aikin zuwa gida uku.
“Kashin farko za a kammala a cikin wata 21, na biyu kuma a cikin wata 23, sai kashi na uku da za a kammala gayan a wata 33,” inji ministan, wanda ya ce an bayar da aikin ne ga kamfanonin Messrs Saipem SPA da kuma Saipem Contracting Limited.
Game da aikin gyaran Matatar Mai ta Fatakwal da a aka bayar tun da farko, Sylva ya ce ’yan kwangilar sun riga sun fara aiki bayan sun karbi kafin alkalami.
“An fara aikin gyaran Matatar Mai ta Fatakwal bayan an ba ’yan kwangilar kashi 15 cikin 100 na kudin aikin.
“Zaman namu ya kuma amince a rika bayar da bayanai daga lokaci zuwa lokaci, saboda haka nan gaba za mu je rangadi a matatar tare da ku,” a cewarsa ga manema labarai bayan taron.
A watan Maris ne Majalisar Zartarwar ta amince da kashe Dala biliyan 1.5 domin gyaran matatar, wadda ita ce mafi girma a Najeriya.
Kudaden shigan Kamfanin NNPC da kasafin kudi da kuma rance da bankin Afreximbank ne dai ake amfani da su wajen gyaran matatar.