Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman Kan Kararraki, Mista Okoi Obono-Obla jiya ya ce kwanannan Gwamnatin Tarayya za ta kwace kangon gidajen da ba mazauna cikinsu a birnin tarayya na Abuja.
Obono-Obla wanda ya yi furucin yayin da ya karbi tawagar kungiyar da ke kamfe din ’Yan Najeriya su tirjewa cin hanci wato “Say No Campaign” ta kai masa ziyara a Abuja.
Ya jaddada bukatar samun hadin kai tsakanin kungiyoyi da gwamnati don samun nasarar gano gidajen da aka mallaka da kudin haram.
“Ya zama wajibi mu karbe gidajen mu sayar da su mu saka kudin cikin ilimin ’ya’yanmu”. Inji shi
Mai Taimaka wa Shugaban Kasar na Musamman ya bayyana cewa ofishinsa a shirye yake ya hada gwiwa da duk wata kungiya da ke goyon bayan yakin da gwamnati take yi da cin hanci da rashawa.