✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta kafa kotunan musamman kan kalaman kiyayya

Bangaren Shari’a da na Zartarwa na Gwamnatin Tarayya da na jihohi za su kafa kotunan musamman da za  su rika gudanar da shari’ar laifukan da…

Bangaren Shari’a da na Zartarwa na Gwamnatin Tarayya da na jihohi za su kafa kotunan musamman da za  su rika gudanar da shari’ar laifukan da suka shafi kalaman kiyayya da satar mutane da kuma ta’addanci.
Wannan shi ne kudurin da aka cimma a taron da aka gudanar kan tsaron kasa a ranar Alhamis din da ta gabata kamar yadda sanarwar da Babban Mai Taimakawa Mukaddashin Shugaban Kasa Kan Kafafen Yada Labarai da Wayar Da Kai, Laolu Akande ya raba wa manema labarai a yau.
Akande ya ce Gwamnatin Tarayya za ta tallafawa gwamnatocin jihohi da tsarin yadda za su kafa kotunan da kuma yadda za su tafiyar da su.
“Membobin kwamitin zartarwa sun bukaci a dauki matakan gaggawa don kamawa tare da gurfanar da masu aikata laifin satar mutane da ta’addanci da kuma wadanda suke yin kalaman kiyayya. Don cimma wannan buri an cimma matsaya kan kafa kotunan musamman kuma aka amince cewa bangaren shari’a da na zartarwa da gwamnatocin jihohi su yi aiki tare wajen kafa kotunan”. Inji shi.